An kone 'yan 'yahoo' biyu, wata bokanya da mai garkuwa da mutane

An kone 'yan 'yahoo' biyu, wata bokanya da mai garkuwa da mutane

Rahotanni sun kawo cewa fusatattun matasa a garin Otuo da ke karamar hukumar Owan na jahar Edo sun babbaka wasu mutane hudu a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu.

An tattaro cewa uku daga cikin wadanda aka babbaka na da hannu a kisan wata yar shekara 17, Ohiole Glory wacce ta kasance daliba a kwalejin Azama, Otuo.

An rahoto cewa mutum na hudun ya kasance madugun masu garkuwa da mutane kuma dan fashi da makami wanda ake kira da Lukman.

Majiyoyi sun ce wacce aka halakan ta fito ne daga yankin Ikhueran Quarters, Iyeu Otuo sannan cewa ana sanya ran za ta rubuta jarrabawarta na WAEC da NECO a wannan shekarar.

An kone 'yan 'yahoo' biyu, wata bokanya da mai garkuwa da mutane
An kone 'yan 'yahoo' biyu, wata bokanya da mai garkuwa da mutane
Asali: Facebook

An cire wasu muhimman sassa na jikin yarinyar a lokacin da aka gano gawarta.

Baya ga kashe wadanda ake zargin, an kona wasu gidaje mallakar iyalansu.

Majiyoyi sun bayyana cewa wacce aka halakar na zama ne a gida guda da biyu daga cikin wadanda ake zargin a Ikhueran Quarters Iyeu Otuo.

Wata majiyar kuma ta ce an yaudare ta ne zuwa dajin mazan inda suka kashe ta sannan aka cire wasu muhimman sassa na jikinta.

Majiyar ta ce an kama wani da ake zargi wanda aka fi sani da No Fuck Up ta hanyar bincike sannan ya ambaci sunayen abokan ta’asarsa bayan ya sha mugun duka.

An kawo cewa an ja shi zuwa hedkwatar yan sanda da ke Otuo sannan aka kashe shi a gaban jami’an yan sanda da kuma cinna wa gawarsa wuta.

Sannan cewa aka kama mutum na biyu yan sa’o’i bayan nan inda shima aka cinna masa wuta.

KU KARANTA KUMA: Yaki da rashawa: Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 160 ga wata Mata da abokanta 3

An tattaro cewa daga bisani sai aka sake kama mutum na uku sannan bayan tambayoyi, ya bayyana cewa wata bokanya mace daga jahar Kogi ce ta tura su.

An rahoto cewa ya fada masu cewa ya kamata a yi masu asiri ne da sassan jikin yarinyar.

An je har gidanta aka kama ta, sannan aka kashe ta tare da cinna mata wuta.

Da aka tuntube shi, kwamishinan yan sandan jahar Edo, Jimeta Lawan ya ce DPO din yankin ya sanar dashi lamarin.

Lawan ya ce jami’an sashin binciken laifuffuna na gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel