Na ji Obaseki na fadin a kashe Oshiomhole – Okosun

Na ji Obaseki na fadin a kashe Oshiomhole – Okosun

Tsohon kakakin majalisar dokokin jahar Edo kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Thomas Okosun, ya yi martani ga rikicin da ke wakana a tsakanin Adams Oshiomhole da Gwamna Godwin Obaseki.

Da yake magana a shirin Channels TV na Sunday Politics, Okosun ya yi zargin cewa Obaseki ya bayar da umurnin kashe Oshiomhole.

“Kafin yanzu, Gwamnan ya yi barazanar cewa a duk lokacin da Oshiomhole ya zo jahar Edo, ya bayar da umurnin gasa masa aya a hannu.

Na ji Obaseki na fadin a kashe Oshiomhole – Okosun
Na ji Obaseki na fadin a kashe Oshiomhole – Okosun
Asali: UGC

"Abunda kuka gani jiya ya kasance wani yunkuri ne na aiwatar da wannan umurnin da Gwamnan ya bayar na gasa wa Adams Oshiomhole aya a hannu. Burinsa shine a kashe shi,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ya ji da kunnensa da Obaseki ke fadin a kashe Oshiomhole, Okosun ya amsa ta hanyar bayar da tabbaci.

“Ina tsaye kan zargina; Ina tsaye kan haka. Kwarai, na ji Obaseki na fadin cewa a gasa masa aya a hannu. Kwarai, na ji. Yana a bidiyo, yana a ko ina,” in ji Okosun.

Da yake martani ga harin da aka ce an kaiwa Oshiomhole yayinda ya ziyarci mahaifarsa a jahar Edo, Okosun ya bayyana cewa ba don jami’an tsaro sun shiga lamarin ba, da an kashe Shugaban jam’iyyar na APC na kasa.

KU KARANTA KUMA: Mawaki Nazifi Asnanic ya shiga sahun fitattun mutanen 10 a jahar Kano

A wani labarin kuma mun ji cewa a ranar Lahadi, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya zargi tsohon Mai gidansa wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, da yin abubuwan da ya ga dama.

Mai girma Godwin Obaseki ya bayyana cewa Adams Oshiomhole ya na abubuwansa da gadara, ganin cewa ya ziyarci Edo ba tare da ya sanar da gwamnati game da zuwansa ba.

Gwamnan ya shaidawa ‘Yan jarida wannan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya kawo masa ziyara ta musamman har gida.

Godwin Obaseki ya ce idan har da mutunci, ya kamata ace tsohon gwamna Adams Oshiomhole ya sanar da gwamnatin jihar Edo cewa zai shigo jihar, ba kawai ya zo kwatsam ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng