Barawo ya sha ashariya a wajen 'yan sanda bayan ya arce da jakar kudin da suka tara na cin hanci

Barawo ya sha ashariya a wajen 'yan sanda bayan ya arce da jakar kudin da suka tara na cin hanci

- An yi wani abu da yayi kama da dirama tsakanin ‘yan sanda da wani barawo a kan babbar hanyar Nairobi zuwa Meru

- Barawon ya fito daga daji ne kwatsam inda ya kwace jakar kudin cin hancin da ‘yan sandan suka tara

- Tuni barawon ya fada cikin dajin da ke kusa wanda dama daga shi ya fito, ‘yan sandan kuwa suka bi shi da zagi don ba zasu iya kamo shi ba

An yi wani karamin lamari da yayi kama da almara a ranar Laraba, 19 ga watan Fabrairu tsakanin ‘yan sanda da kuma wani barawo. Barawon ya wabce jakar da ‘yan sandan suka zuba cin hancin da suka samu a kan titi sannan ya shige daji da gudu.

Kamar yadda jaridar Tuko.co.ke ta ruwaito, lamarin ya faru ne kusa da wani babban shago na Kathegeri da ke babbar hanyar Nairobi zuwa Meru.

Jaridar The Pulse.ng ta bayyana cewa barawaon ya fito ne daga cikin daji, inda ya kwace kudin da ‘yan sandan suka tara sannan ya shige dajin da ke kusa dasu a guje.

Jaridar Nairobi News ta ruwaito cewa wani ganau ba jiyau bane ya sanar da cewa ‘yan sanda biyu ne mace da namiji ke kan titin a yayin da aka musu fashin.

KU KARANTA: Amarya ta yafe sadakin aurenta, amma ta ce ango yayi mata alkawarin babu shi babu kara mata kishiya

“Akwai wata hanya ce da ta hada titin da dajin. Ta nan kuwa ‘yan sandan ke tsaye amma ta bangaren titin. Daga ciki barawon ya bayyana tare da wabce jakar kudin cin hanci da suka tara. Ganin ba zasu iya kamo shi bane yasa suka dinga zagin shi,” ganau din ya sanar.

Wanda lamarin ya faru a gaban shi ya ce dan sandan ya yi yunkurin damko barawon amma hakan bai samu ba saboda yanayin wajen. Hakazalika ‘yan sandan rike suke da kulki ba bindiga ba. Hakan ne kuwa yasa suka dinga dura mishi zagi.

Kafin su rasa kudaden da suka tara, jami’an ‘yan sandan sun dinga tsayar da motoci inda suka dinga karbar kudi daga wajen mutane. Cikin kuwa sa’o’i kasa da biyar barawon ya kwace ‘gumin’ ‘yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel