Jihohin Najeriya za su samu karin kason kudi bayan karin VAT – Inji AGF

Jihohin Najeriya za su samu karin kason kudi bayan karin VAT – Inji AGF

Akantan Janar na kasa, Ahmed Idris, ya bayyana cewa jihohi da kananan hukumomin Najeriya za su samu karin kudi daga asusun gwamnatin tarayya nan gaba.

An ci ma wannan matsaya ne bayan karin kudin harajin VAT kayan masarufin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi daga 5% zuwa 7.5%.

Ahmed Idris ya bayyana wannan ne a Ranar Laraba, 19 ga Watan Fubrairun 2020, a lokacin da ya zanta da Manema labarai a wajen wani taro na kwamitin FAAC.

Kamar yadda Hukumar dillacin labarai ta kasa watau NAN ta bada rahoto, an yi wannan zama ne a Legas domin tattauna batun kason kudin da gwamnati ta ke samu.

Gwamnatin tarayya ta na kokarin ganin ta raba kafa wajen fadada samun kudin shiga domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya da ya dogara da danyen man fetur.

KU KARANTA: Wani Gwamna ya tsere daga Jiharsa ya tare a Birnin Tarayya

Jihohin Najeriya za su samu karin kaso bayan karin VAT – Inji AGF
Gwamnatin Buhari ta kara harajin wasu kayan masarufi a 2020
Asali: Twitter

“Za ku ga tasirin karin VAT ne daga Wata mai zuwa saboda karin ya soma aiki ne daga Ranar 1 ga Watan Fubrairu. Jihohi da kananan hukumomi za su ga kari.”

Mista Ahmed Idris ya kara da cewa: “Gwamnatin tarayya ta na da 15%, Jihohi su na da 50%, sai kuma kananan hukomomi za su samu 35% daga harajin na VAT.”

“Duk za ku ga wannan a watanni masu zuwa. Ina sa ran cewa daga Watan gobe, za ku ga karin harajin VAT da aka yi a cikin kudin shigan gwamnatin tarayya.”

Babban Akawun gwamnatin kasar ya tabbatar da cewa su na kokarin habaka karfin samun kudin shiga. AGF ya yi kira ga kwamishinonin kudi su yi na su kokarin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng