Tattalin arziki: Danyen man Najeriya zai kare nan da shekaru 49 Inji DPR

Tattalin arziki: Danyen man Najeriya zai kare nan da shekaru 49 Inji DPR

Arzikin danyen man Najeriya da ke ajiye wanda ya kai ganga biliyan 37 zai kare nan da shekaru 49 masu zuwa inji hukumar DPR mai kula da arzikin mai na kasa.

DPR ta bayyana cewa a duk shekara Najeriya ta kan hako 2% na danyen man da ke kwance. Wannan ya sa nan da wasu shekaru za a hake man da kasar ta tara.

A shekarar 2014, adadin gangunan danyen man da Najeriya ta adana ya kai ganga biliyan 37.45, a shekarar 2015, adadin danyen man ya ragu zuwa ganga biliyan 37.06.

DPR ta ce a 2016, Najeriya ta na da gangar danyen mai biliyan 36.74 a adane. An yi sa’a yawan man da kasar ta ke da shi ya karu daga 36.74 zuwa 36.97 a shekarar 2017.

“Duk shekara Najeriya ta na hako 2.04% na danyen man ta, sannan lokacin da za a dauka kafin man da ke kasa ya kare kar-kaf shi ne shekaru 49.03.” Inji hukumar.

Hakan na nufin a farkon shekarar 2070 rijiyoyin da ke dauke da man Najeriya za su kafe. Hukumar DPR ta gane abin da kasar ta ke sha ne bayan ta yi wani liissafi.

KU KARANTA: An gano wasu matatun da ba su da lasisi a Najeriya

Tattalin arziki: Danyen man Najeriya zai kare nan da shekaru 49 Inji DPR
Najeriya ta na cikin kasashen da ta ke da arzikin mai.
Asali: UGC

An raba adadin man da kasar ke sha a shekarar 2018 da adadin abin da ya rage a cikin rijiyoyin man kasar a farkon shekarar 2019, wannan ya nuna abin da aka ci.

Hukumar DPR ta ce wannan alkaluma sun taimaka wajen nuna abin da ake hakowa daga cikin rijiyoyin man Najeriya. Sai dai ana rage amfani da fetur a Duniya

Da aka raba yawan abin da ke rijiyoyin kasar da kuma abin da aka hako a shekarar 2018, sai ya nuna lokacin da ake sa ran danyen man kasar zai kare gaba daya.

Dole a kara kokari wajen gano wasu rijiyoyi da kuma kara haki idan har gwamnati ta na so ta cin ma burinta na kara yawan man da ta ke hakowa a kowace rana.

Gwamnatin Najeriya ta na son a rika hako ganga miliyan hudu a kullum, sannan kuma ta na so ace akwai akalla ganguna biliyan 40 da ke kwance a rijiyoyin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel