Ma'aikatan Hukumar NSCDC sun gano gonar wiwi a Makarantar Anambra

Ma'aikatan Hukumar NSCDC sun gano gonar wiwi a Makarantar Anambra

Mun samu labari cewa jami’an hukumar NSCDC a Najeriya, sun gano wata katuwar gona da aka noma tabar wiwi a wata makaranta da ke jihar Anambra.

A Ranar Talata, 18 ga Watan Fubrairun 2020 ne jami’an na NSCDC su ka yi nasarar gano wannan gona. Yanzu an cafke wanda ake zargi da mallakar gonar.

Shugaban hukumar NSCDC na jihar Anambra, David Bille, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa wani mutumi mai suna Obi Okafor ake tuhuma da wannan aiki.

Obi Okafor mai shekaru 45 a Duniya, shi ne wanda ake zargi da shuka tabar wiwi a gonar da ke cikin wannan Makaranta inji hukumar NSCDC na jihar.

An kama Okafor ya dabawa Mai gadin Makarantar adda bayan rikici ya barke tsakaninsu, sakamakon gano abin da mutumin ya ke yi a cikin gonar.

KU KARANTA: Jami'in 'Dan Sanda ya bindige wani Mutumi saboda N50

Ma'aikatan Hukumar NSCDC sun gano gonar wiwi a Makarantar Anambra
Jami'an NSCDC za su mika wanda aka kama gaban NDLEA
Asali: UGC

“Ainihin Obi Okafor mutumin Kauyen Urofo ne a Garin Nri da ke karamar hukumar Anaocha a jihar Anambra. An yi ram da shi ne da karfe 12:00 na rana.”

“An kama wanda ake zargi da laifin kai wa wani ‘Dan shekara 71 mai suna Mathias Ajoagu, hari da gatari. Wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa da kansa."

"Shi da kanshi ya jagoranci Jami’an tsaro zuwa inda ya ke shuka tabar a gonar." Mista David Bille ya yi wa Manema labarai wannan bayani ne Garin Awka.

Daga cikin abubuwan da aka samu a hannunsa akwai adda, ganyen tabar wiwi da sauransu. Yanzu an fara bincike, kuma za a mika shi gaban NDLEA nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel