Yan majalisa sun sha kuka da hawaye kan kashe-kashen Katsina

Yan majalisa sun sha kuka da hawaye kan kashe-kashen Katsina

Zauren majalisar dokokin jahar Katsina ya zama wajen kuka da hawaye a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu kan kisan kwanan nan na sama da mutane 30 da aka yi a kauyuka da ke karamar hukumar Batsari na jahar.

Alhaji Jabiru Yau-yau, mamba mai wakiltan mazabar Batsari ya gabatar da lamarin a zauren cikin lamuran da ke bukatar kulawar gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mamba mai wakiltan mazabar Jibia, Alhaji Mustapha Yusuf, ne ya bude kofar kuka yayinda ya ke bayar da gudunmawarsa kan lamari daga nan sai sauran yan majalisar suka taya shi zubar da hawaye kan kashe-kashen.

Yan majalisa sun sha kuka da hawaye kan kashe-kashen Katsina
Yan majalisa sun sha kuka da hawaye kan kashe-kashen Katsina
Asali: Facebook

“Wannan lamarin abun tsoratarwa ne saboda bamu san abun da zai iya sake faruwa ba a wannan wajen.

“An kulle mutane da dama sannan aka kona su kurmus. Mutanen kauyukan sun tsere zuwa wurare daban-daban saboda tsoron abun da ke duhu.

“Haba, wani irin mummunan abu ne wannan; wannan abun bakin ciki ne, yadda aka kashe rayukan mutane kamar dabbobi,” in ji Yusuf cikin hawaye.

An tattaro cewa jama’a da ke a zaman majalisar ciki harda wasu manema labarai da ke nadar zaman sun samu raunin zuciya sannan suma suka bi sahu inda aka koka tare da su kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin yaye sabbin jami’an EFCC a Kaduna

Yau-yau, wanda ya fara kukan, ya roki gwamnatocin jiha da na tarayya da su inganta tsaro sannan su samar da kayayyakin agaji ga mutane a kauyukan Dankar da Tsanwa.

Ya yi korafin cewa mutanen sun bar gidajensu sannan wadanda suka dawo basu da abinci da wajen kwana saboda yan bindigan sun lalata masu gidajensu.

A wani labari na daban mun ji cewa wasu makasa sun hallaka mataimakiyar diraktar gudanarwan fadar shugaban kasa, Laetitia Dagan, a gidanta dake Abua, fadar shugaban kasa ta bayyana.

Mataimakin dirkatan labaran fadar shugaban kasa, Attah Esa, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya sake inda ya ce an kashe Dagan ne misalin karfe 11 na daren Litinin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel