Akwai abin ban dariya a tafiyar APC – Tsohon Sakataren Gwamnati, Lawal

Akwai abin ban dariya a tafiyar APC – Tsohon Sakataren Gwamnati, Lawal

Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, ya yi wata doguwar hira da Premium Times inda ya tattauna game da batun gwamnati, siyasar APC da shugabancin kasa.

Babachir David Lawal ya nuna cewa ya na ganin darajar Bisi Akande a matsayinsa na Dattijo, amma ya nuna shakkun samun nasara game da aikin da kwamitinsa zai yi na sulhu a APC.

Injiniya Babachir Lawal ya ce: “APC ta na da abin ban dariya, yanzu Shugaban jam’iyya da mutanensa sun dakatar da mataimakan APC na Arewa da shugaban Arewa maso Yamma.”

“Sakataren jam’iyya wanda ya fito daga Arewa, ya zama gwamnan Yobe. Har yanzu da mu ke magana babu wani kokarin kirki na maye gurbinsa.” Lawal ya ce an yi wa Arewa gibi a APC.

Bayan haka, har yanzu babu sabon mataimakin shugaban jam’iyya daga Kudu da kuma mai binciken kudi. Akwai kuma irinsu Ibekunle Amosun da Rochas Okorocha da aka dakatar.

KU KARANTA: An bukaci a damke Shugaban APC saboda wasu kalamai da ya yi

Akwai abin ban dariya a tafiyar APC – Tsohon Sakataren Gwamnati, Lawal
Babachir Lawal ya koka a kan yadda Oshiomhole ya kori manyan 'Yan APC
Asali: UGC

Ganin yadda APC ta rasa Ribas, Zamfara, da wasu Jihohi, Lawan ya nuna cewa dole sai Adams Oshiomhole da mutanesa sun kara kokari wajen ganin jam’iyyar ba ta fadi zabe a 2023 ba.

Tsohon SGF din ya kuma yi magana game da kwaskwarimar da Majalisa za ta yi wa tsarin mulki. A na sa shawarar, zai yi kyau Najeriya ta koma amfani da Majalisa guda domin rage kashe kudi.

A kan rikicin Boko Haram, Lawal ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne ace abubuwa su na tabarbarewa. Lawal ya ce an samu cigaba, kuma shugaban kasa ya san yadda za a kawo gyara.

Babachir Lawal ya kuma bayyana cewa gwamnoni ne ke hana ruwa guda a Najeriya, ya kira su kaskoki wanda ke karbar kudi daga asusun tarayya, su batar ba tare da sun yi wani aiki ba.

A daidai wannan lokaci sai aka ji cewa a Osun, Gboyega Oyetola ya sayo motocin N260m yayin da tsofaffin Ma’aikata ke bin bashin kudinsu na fansho da sallamar aiki tun a gwamnatin baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel