Shehu Sani ya yi magana game da jita-jitar kai wa Amaechi hari a jirgin kasa

Shehu Sani ya yi magana game da jita-jitar kai wa Amaechi hari a jirgin kasa

Sanata Shehu Sani ya yi magana game da rahotannin da su ka rika yawo na cewa Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya sha da kyar a hannun ‘Yan bindiga.

Tsohon ‘Dan majalisar ya maida martani ne ga rade-radin cewa ‘Yan bindiga sun kai hari a tashar jirgin kasan da ke Garin Kaduna, inda aka ce har Ministan ya na ciki.

Shehu Sani ya yi magana cikin ba’a, ya na nuna cewa bai kamata a ga laifin Mai girma Ministan sufurin idan ya tserewa ‘Yan bindiga domin ya ceci rayuwarsa ba.

Sani ya fito shafinsa na Tuwita a Ranar Litinin ya na cewa: “Gaskiya ne ko ma dai karya, ka da ku ga laifin Minista idan ya sheka a guje kamar wani Usain Bolt.

Usain Bolt ‘Dan wasan tsere ne wanda ya na cikin wadanda su ka fi kowa gudu a tarihin Duniya.

KU KARANTA: Kasar Libya ta hana Najeriya zaman lafiya ba kowa ba - Buhari

Sanatan ya kuma kara da cewa: “Wadannan ‘yan bindiga ba su san wata Majalisar zartarwa ta FEC ba. Toh, shin idan kai ne ba za ka gudu ba, wai don ka na Minista?”

Ministan sufurin kasar ya karyata cewa ya an kai masa hari, a cewarsa ya na barci salin-alin a Kaduna aka rika kiransa a wayar tarho bayan rade-radin ya shiga ko ina.

A baya Sani ya taba bada labarin yadda ya ga wani babban Soja a jirgin kasa duk da a lokacin Sojoji su na ikirarin sun lallasa Miyagun da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Sani ya wakilici Kaduna ta tsakiya ne a majalisar dattawan Najeriya a majalisa ta takwas, kuma ya kan fito ya yi magana a shafukansa na Tuwita da Facebook bini-bini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel