Wajibi ne Adam Zango ya bi dokokin fina-finan Kano – Afakallahu

Wajibi ne Adam Zango ya bi dokokin fina-finan Kano – Afakallahu

Hukumar tace fina-finai da dab'i'u ta jahar Kano ta bayyana cewa dole sai tsohon shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Adam A. Zango ya bi dokokinta idan har yana so ya je jahar domin gudanar da harkokin fim.

A ranar Juma'a da ya gabata ne Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ya yi wa masoyansa na jahar Kano albishir din cewa zai je jahar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau' wanda ake haskawa a film house cinema da ke Shoprite.

Bayan wannan sanarwar ne kuma sai ga wata sanarwa daga shugaban hukumar tace fina-finai a jahar Kano, Isma'ila Na'abba Afakallahu, inda ya ke cewa sai sun kama Adam idan har ya shigo jahar.

Sai dai Afakallahu ya ce ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa, shafin BBC ta ruwaito.

Wajibi ne Adam Zango ya bi dokokin fina-finan Kano – Afakallah
Wajibi ne Adam Zango ya bi dokokin fina-finan Kano – Afakallah
Asali: Facebook

Afakallahu ya ce: "Idan zuwa zai yi ya kalli fim kawai ya tafi shikenan, akwai wadanda ba su da rajista kuma suke zuwa su yi kallon su tafi babu ruwanmu da su.

"Kwanakin baya wannan hukumar ta yi kokarin tantancewa da tsafetace masu ruwa da tsaki a wannan harka kamar yadda doka ta ba ta dama."

Afakallahu ya kara da cewa Zango bai da rijista da hukumar.

"An samu mafi yawa daga cikinsu sun zo sun yi amma shi (Adam Zango) yana cikin wadanda ba su yarda su yi hakan ba, har ma ya ce ya fita daga tsare-tsarenmu."

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole a sallami shugabannin tsaro – Yan majalisar tarayya

Kan cewa ko hakan ba zai zama tauye hakkin Adamu wanda kundin tsarin mulki ta bashi, Afakallah ya ce: "Don an ba ka 'yanci ai kuma akwai inda 'yancin wasu za ka taka."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng