Tarbiyyantar da Mata da Yara zai yi maganin shaye-shaye al'umma – Rijiyar-Lemu
Fitaccen Shehin addinin Musulunci kuma Malamin Jami’a, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi magana game da harkar shaye-shaye a cikin al’umma.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, Shehin, ya bayyana cewa bada tarbiyyar Musulunci ga kananan yara da kuma mata zai taimaka wajen maganin matsalar.
Malamin addinin ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya gabatar da wata takarda kwanan nan a kan matsayar Musulunci wajen magance matsalar shaye-shaye.
Daily Trust ta ce Sani Umar Rijiyar Lemu da sauran Masana sun gabatar da takardu ne a wajen wani taron kasa da aka shirya domin yaki da shan kayan maye.
Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya ce Mata su ne ginin duk wani gida da kuma al’umma don haka dole a ba su fifiko saboda kusancinsu da kananan yara.
KU KARANTA: 'Yan Najeriya fiye da miliyan 10 su na shaye-shaye - Bincike
Tarbiya da gyaran al’umma sun fara ne tun daga gida a wajen Mahaifiya don haka dole Uwa ta zama mai kyakkawar dabi’a, ya ce haka malaman makaranta.
Dr. Sani Rijiyar Lemu ya nuna cewa ana fuskantar matsalar shaye-shaye har a Makarantu, inda ake samun Malaman da ke bada tarbiya, su na shaye-shaye.
Malamin ya ce addinin Musulunci ya yi hannun riga da giya domin kuwa kayan maye su ne silar duk wata tabarbarewar da ake fuskanta yau a cikin al’umma.
“Mata su ne katangar al’umma, amma yanzu sun fi kowa shan kwayoyi, ta ya irin wannan mace za ta yi wa yara tarbiya har su zama nagari?” Inji R/Lemu.
Malamin ya yi kira ga jama’a su zama masu halin kirki tare da kiran hukunta masu dillacin kayan maye. “Duk abu mai sa maye, haramun ne a Musulunci.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng