Yanzu Yanzu: Buhari ya bayyana matsayarsa a kan harin Katsina

Yanzu Yanzu: Buhari ya bayyana matsayarsa a kan harin Katsina

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da yan fashi suka kai kan manoma a kauyukan Damkal da Tsanwa da ke karamar hukumar Batsari a jahar Katsina

- Buhari ya ce kashe mutane da sunan ramuwar gayya ba abun yarda bane

- Ya bukaci shugabanni da hukumomin garuruwa da su cigaba da kokarinsu na hada kai da hukumomin doka da ke maganin yan bindiga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da yan fashi suka kai kan manoma a kauyukan Damkal da Tsanwa da ke karamar hukumar Batsari a jahar Katsina, cewa kashe mutane da sunan ramuwar gayya ba abun yarda bane.

Da yake martani ga lamarin wanda a ciki aka kona gidaje da dama da kuma kashe mutane a karshen mako, Shugaban kasar a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairu ya yi gargadin cewa “babu wani a kasar nan da ke da ikon daukar doka a hannu a matsayin kare kai ko ranuwar gayya. Idan mazauna garuruwa suka kama yan bindiga toh su mika su ga hukumomin tsaro mainakon daukar doka a hannu da ka iya haifar da ramuwar gayya.”

Ya bukaci shugabanni da hukumomin garuruwa da su cigaba da kokarinsu na hada kai da hukumomin doka da ke maganin yan bindiga, wanda hakan kan kawo zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya.

KU KARANTA KUMA: Hatsarin mota: Mutane 22 sun mutu, 11 sun samu rauni a Katsina

“Ya zama dole a bari hukumomi su yi bincike da magance kowani lamari da ya afku. Tashin hankali bai da mazauni a kasa mai mutunci,” in ji shugaban kasar.

Shugaba Buhari ya yi addu’an Allah ya ba iyalan da suka rasa masoyansu a hare-haren juriya sannan ya yi addu’an Allah ya ji kan wadanda suka rasu.

A wani labarin kuma mun ji cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren din-din-din na ma’aikatar ayyukan a jahar Nasarawa, Alhaji Jibrin Giza, a tsakar daren ranar Asabar.

Kwamishinan yan sanda a jahar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Lafia.

Longe ya fada ma NAN cewa yan bindiga sun sace sakataren din-din-din din daga gidansa a Shabu, wani yanki na Lafia da misalin 12:40 na tsakar dare zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel