Mala Buni ya ce burin ‘Yan takarar 2023 ba zai wargaza Jam’iyyar APC ba
Tun yanzu har ‘Yan siyasa sun fara lissafin zaben 2023 wanda za a fuskanta nan da shekaru uku da rabi masu zuwa. Mai Mala Buni ya tofa albarkacin bakinsa game da batun.
Jam’iyyar APC da PDP su ne manyan wadanda su ke harin kujerar shugaban kasa a 2023. APC za ta so ta cigaba da rike mulki, yayin da PDP kuma ke kokarin komawa kan mulki.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa Malam Nasiru El-Rufa’i da Bola Ahmed Tinubu su na harin 2023, ba wata matsala ba ce.
Alhaji Mai Mala Buni ya yi wannan bayani ne lokacin da ya yi hira da BBC Hausa, inda ya nuna cewa burin ‘Yan siyasa ba zai nakasa tafiyar APC kamar yadda wasu ke tunani ba.
Buni ya ke cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafawa jam’iyyar APC mai mulki tubali mai kyau saboda irin rikon da ya yi wa kasa wanda zai sa APC ta cigaba da mulki.
KU KARANTA: An zargi Shugaban APC da jefa jam'iyya cikin matsala a Bayelsa
A hirarsa da BBC, Mai Mala Buni ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kiran da wasu su ke yi na cewa a mika mulki zuwa Kudancin Najeriya bayan Buhari ya kammala wa’adinsa.
Haka zalika tsohon Sakataren na jam’iyyar APC na kasa, ya yi magana game da siyasar jihar Yobe, inda ya nuna cewa babu wani sabani tsakanin tsohon gwamna da gwamnatinsa mai-ci.
Buni ya ke cewa ‘Yan siyasar Yobe su na da hadin-kai don babu bangaranci tsakanin mutanesa da yaran tsohon gwamna, asali ma ya ce wasu Kwamishoninsa ma ba ‘Yan siyasa ba ne.
Wasu daga cikin Jagororin APC irinsu Babachir David Lawal su na ganin cewa Bola Tinubu ya dace da mulki a 2023. Akwai kuma rade-radin cewa Nasir El-Rufai zai nemi takara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng