Abun da ya sa ba zan daina yin fim ba - Sapna Aliyu

Abun da ya sa ba zan daina yin fim ba - Sapna Aliyu

Fitaciyyar jarumar Kannywood, Sapna Aliyu Maru ta jadadda cewa ba za ta taba yanke alaka da harkar fim ba ko da ta yi aure. A cewarta za ta dunga daukar nauyin shirya finafinai bayan ta yi aure, Mujjalar Fim ta ruwaito.

Jarumar ta yi wadannan jawabai ne a daidai lokacin da wasu ke cewa ta bar Kannywood, ta rungumi harkar kasuwancin ta.

Sapna, wacce tauraruwar ta ta dunga haskawa a shekaru biyu zuwa uku da su ka gabata, ta ce har yanzu ita cikakkiyar jaruma ce a masana'antar shirya finafinan.

Abun da ya sa ba zan daina yin fim ba - Sapna Aliyu
Abun da ya sa ba zan daina yin fim ba - Sapna Aliyu
Asali: Facebook

Sapna ta yi bayyana matsayin ta da cewa, "Ni abin da zan fada, Sapna dai ba ta daina yin fim ba, domin fim sana'a ta ne, babu yadda za a yi na daina yi sai dai idan na yi aure, kuma ko da na yi aure zan ci gaba da yin furodusin kamar yadda na ke yi.

"Illa iyaka dai a yanzu akwai wasu abubuwa da na ke yi da su ka shafi harkar kasuwanci wanda a yanzu su na sa a gaba.

"Kuma ko da aka daina gani na, ina yin furodusin, ba na fitowa ne dai a ciki, don haka ake ganin kamar na daina yi, domin ko rajistar da aka yi a Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano na je na yi a matsayina na furodusa, don haka ka ga ai ni cikakkiyar 'yar fim ce."

Jarumar ta ci gaba da cewa, "Kamar yadda na fada, ina harkar kasuwanci, don haka na kan je na saro kaya na raba ko na zuba a kanti na, don haka sai ya zama babu lokaci a gare ni da zan gudanar da harkar da har zan samu lokacin da wani zai gayyace ni fim ɗin sa, don haka idan na ce zan karɓi aikin mutane, ban san yadda zan yi da su ba."

Fim din Sapna na ƙarshe shi ne 'Wata Rana', wanda ita ce ta shirya shi.

"Ni ce jarumar fim din wanda mu ka yi da Adam A. Zango," inji ta. "Ina ganin ya kai kamar shekara uku yanzu. To tun daga shi sai dai na yi furodusin idan na samu lokaci."

Ko yaya Sapna ta ke kallon harkar fim a yanzu? Sai ta ce, "To wani lokacin dai zan iya cewa daga nesa na ke kallon ta, domin yanzu ba ko yaushe na ke samun lokacin shiga cikin harkar ba. Amma duk da haka, idan na shiga ina ganin ci-gaban ta, domin na kan ga sababbin abubuwa na cigaba.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli: Allah ya warkar da jahar Bayelsa – In ji Diri

"Don haka zan iya cewa harka fim ta na samun cigaba, kuma ina fatan cigaban ya dunga samuwa nan gaba."

Daga karshe, jarumar ta yi fatan samun hadin kan 'yan fim domin a samu cigaba da zaman lafiya mai dorewa a cikin masana'antar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng