Na yafewa Yaran Amosun da su ka jefi Buhari a Abeokuta - Abiodun
Mai girma gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce ya yafewa Sanata Ibikunle Amosun da Magoya bayansa da su ka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta’adi a bara.
Dapo Abiodun ya bayyana cewa ya yi wa tsohon gwamnan da kuma yaran gidansa afuwa na jifar shugaban kasa da tawagarsa da su ka yi a lokacin da ya zo kamfe a Garin Abeokuta.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Kunle Somorin, ya fitar da jawabi a Ranar Laraba, ya ce:
“A wajen taron majalisar zartawa da aka yi a ofishin gwamna, Mai girma gwamna ya tuna da yadda wasu fusatattun ‘Yan APC su ka zo daf da rotse shugaban kasa da duwatsu.”
“Buhari da wasu Jagororin APC har da shugaban jam’iyya, Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu, da Rauf Aregbesola (su na cikin wadanda saura kiris a jefe su)”
KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa ta bayyana wadanda su ka yi wa Buhari ihu a Borno
Gwamna Abiodun ya na mai cewa: “Ba na rike da kowa a zuciya ta” Ya ce: “Duk wadanda su ka jefe mu, su ka duke mu, sun taka irin ta su rawar ganin da Ubangiji ya kaddara.”
Duk da haka: “Mun yafe masu, muhimmin abu shi ne Ubangiji ya sa mun samu nasara.” Abiodun ya ce irin wannan wulakanci ya taimaka masa wajen lashe zaben gwamna.
“Ina tunani hanyar da za mu godewa Ubangiji da ni’imarsa shi ne mu yi aiki. Mutanen jiha sun damka mana amanar jagorantar. Ranar 11 na Fubrairu, ta bar tarihi a tafiyarmu."
A Ranar Talata, 11 ga Watan Fubrairu, aka cika shekara guda da faruwar wannan abin kunya. An yi wannan ne lokacin da ake mikawa Abiodun tutar jam’iyyar APC a jihar Ogun.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng