Sojoji sun sake ragargazan 'yan ta'adda, sun kamo wasu tare da makamai

Sojoji sun sake ragargazan 'yan ta'adda, sun kamo wasu tare da makamai

Rundunar sojin Najeriya ta ce, a cigaba da yaki da ta’addancin da take yi a yankin Arewa maso gabas, ta kara kashe wasu ‘yan ta’addan tare da kama wasu motocinsu, bindigogi da kuma manyan makamai daga hannun ‘yan Boko Haram da ISWAP.

Mai kula da yada labarai na rundunar, Kanal Aminu Iliyasu wanda ya bayyana hakan, ya ce an kama wani mayakin Boko Haram din a raye mai suna Koise Bulama, kamar yadda Sun News Online ta ruwaito.

Ya lissafo makaman da aka kama a tare da su. Sun hada da wata motar yaki, bindigar harbo jirgin sama, bindigogi kirar AK 47 guda biyu, harsasai 141, rigar kare bindiga daya, abu mai fashewa guda daya da sauransu.

Idan bamu manta ba, a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar bayan halartan taron AU na 33 a kasar Habasha.

Sojoji sun sake ragargazan 'yan ta'adda, sun kamo wasu tare da makamai
Sojoji sun sake ragargazan 'yan ta'adda, sun kamo wasu tare da makamai
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Legit.ng ta ruwaito cewa babban mai ba Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Ya ce Shugaba Buhari, ya taso daga Addis Ababa sannan a yanzun nan ya sauka a Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.

Shugaban kasar zai kai ziyarar jaje ne ga gwamnati da mutanen jahar Borno biyo bayan mummunan lamarin da ya auku kwanan nan inda yan ta’addan Boko Haram suka kashe matafiya da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel