Rundunar soji ta jadadda kokarin da take na kama Shugaban Boko Haram

Rundunar soji ta jadadda kokarin da take na kama Shugaban Boko Haram

- Kwamandan rundunar sojin Najeriya, Janar Abdul Kalifa Ibrahim, ya bayar da tabbacin cewa sojoji sun jajirce a kokarinsu na kamo Shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, Shekau

- Ibrahim ya ce da izinin Allah za su cimma nasara a yakinsu da yan ta'adda

- Ya yi bayanin cewa an zuba wata bataliya a wannan yankin kusa da Mainok, yayinda hedkwata ke a Jakana domin ba jami'an sojin da ke yankin damar yin sintiri da kuma hana ayyukan yan ta'adda

Wani kwamandan rundunar sojin Najeriya, Janar Abdul Kalifa Ibrahim, ya bayar da tabbacin cewa sojoji sun jajirce a kokarinsu na kamo Shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, Shekau, jaridar Vanguard ta ruwaito.

“Da izinin Allah, za mu samu nasara,” in ji shi.

Janar Ibrahim ya yi magana ne a wata hira da muryar Amurka a ranar Talata.

Rundunar soji ta jadadda kokarin da take na kama Shugaban Boko Haram
Rundunar soji ta jadadda kokarin da take na kama Shugaban Boko Haram
Asali: Facebook

Da yake magana kan sabon harin da aka kai hanyar Damaturu- Maiduguri, kwamandan sojin ya ce: "zancen gaskiyashine cewa mutane sun yi zarya a hanyar nan ba tare da matsala ba amma na fada maku, wadannana yan ta'addan a suka rage yan tsiraru ne. Amma duk da haka akwai dabarun da hukumomin tsaro suke yi a yanzu kan haka kuma da izinin Allah, za mu magance wannan matsalar."

Ya yi bayanin cewa an zuba wata bataliya a wannan yankin kusa da Mainok, yayinda hedkwata ke a Jakana domin ba jami'an sojin da ke yankin damar yin sintiri da kuma hana yan ta'addan aiwatar da ayyukansu.

KU KARANTA KUMA: Sanata Elisha Abbo ya siyi timatirin N100 kan N50k a hannun yar shekara 4 da ke talla a Adamawa

Ba wai bamu da kayayyakin aiki bane, amma muna bukatar karin kayayyaki," in ji shi. da aka tambaye shi kan yiwuwar kama Abubakar Shekau, ya ce: "Muna aiki kan haka kuma idan Allah ya yarda za mu cimma nasara.

A halin da ake ciki, mun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta musamman mai suna Operation Safe Haven sun kama wani wanda ake zargin dan Boko Haram ne. Rundunar ne masu kula da zaman lafiya a wasu sassa na jihar Filato, Bauchi da kuma jihar Kaduna.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Augustine Agundu, ya bayyana cewa wanda ake zargin mai suna Umar Musa Tello an kama shi ne a wajen caca da ke kauyen Zawurna a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, kamar yadda jaridar Daily Trust at tabbatar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng