An gano motocin alfarma 100 na biliyoyin Naira da tsohon gwamna Yari ya karkatar

An gano motocin alfarma 100 na biliyoyin Naira da tsohon gwamna Yari ya karkatar

Kwamitin bin diddigi domin tabbatar da aiyukan gwamnati a jihar Zamfara ya gano wasu motocin alfarma fiye da 100 da tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, ya saya a kan kudi biliyan N8.4 ya raba ga 'yan uwa da abokansa.

A cikin wata sanarwa da ta fito ranar Talata daga ofishin Zailani Bappa, mai taimaka wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a kan harkokin sadarwa da yada labarai, ya bayyana cewa shugaban kwamitin, Ahmed Gusau, ne ya sanar da hakan a cikin rahoton 'somin tabi' da kwamitin ya mika wa gwamnan.

A cewar rahoton, tsohuwar gwamnati a karkashin Yari ta gaza nuna inda fiye da motoci 100, kwatankwacin kaso 66% na motocin da gwamnatin jihar ta mallaka, suke bayan karewar wa'adinta.

Kazalika, kwamitin ya ce ya gano wasu kudi kusan miliyan N35 da gwamnatin Yari ta ki mayar wa wasu maniyyata zuwa aiki Hajji da ba a samu damar tashi dasu zuwa Saudiyya ba a shekarar 2012.

Ahmed Gusau ya roki gwamna Matawalle da ya dauki nauyin maniyyatan zuwa kasar Saudiyya domin gudanar aikin Hajji mai zuwa.

An gano motocin alfarma 100 na biliyoyin Naira da tsohon gwamna Yari ya karkatar
Gwamna Bello Matawalle
Asali: Facebook

A bangaren tsarin ciyar da daliban makarantun firamare, Ahmed Gusau ya bayyana cewa babu tsoron Allah a cikin harkar, saboda abincin da ake bayar wa bai dace da mutane ba ko kadan.

DUBA WANNAN: Abinda muka tattauna da Dame Patience a Villa yayin ganawarmu - Aisha Buhari

"Wani ko karensa ba zai iya bawa irin abincin da suke bawa yaran jama'a ba a makarantun gwamnati.

"Bayan rashin ingancin abincin da suke bawa daliban, suna kara yawan daliban. Akwai makarantar da shugabanta ya yi ikirarin cewa yana ciyar da dalibai 700 yayin da ko dalibai 50 ba ya ciyar wa," a cewar Ahmed Gusau.

Da yake karbar rahoton kwamitin, gwamna Matawalle ya yi musu godiya tare da daukan alkawarin cewa zai duba rahoton a tsanake tare da zartar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel