Sudan: Al-Bashir zai fuskanci ICC bisa zargin kashe Bayin Allah

Sudan: Al-Bashir zai fuskanci ICC bisa zargin kashe Bayin Allah

Mahukuntan kasar Sudan sun amince cewa wadanda ake nema a gaban babban kotun ICC ta Duniya, za su bayyana a gabanta.

An dauki wannan mataki ne bayan wani zaman sulhu da aka yi tsakanin gwamnatin Sudan da kuma ‘Yan tawayen Yankin Darfur.

BBC ta bayyana cewa wannan yarjeniya da aka cin ma, zai sa a tasa keyar tsohon shugaban kasa Omar Al-Bashir zuwa kotun na ICC.

Ana zargin Omar Al-Bashir da laifuffukan yaki wanda su ka hada har da kashe mutane 300, 000 a lokacin da rikici ya barke a Darfur.

Wannan abu ya faru ne a 2003 lokacin da shugaban ya ke rike da kasar Sudan. Al-Bashar ya hau kujera ne a 1989 bayan juyin-mulki.

“Ba za a samu adalci ba muddin ba mu dinke baraka ba.” Inji Mohammed Hassan Eltaish wanda ya ke magana a madadin kasar Sudan.

KU KARANTA: Abin da ya sa ba mu goyon-bayan Amotekun – Inji Miyetti Allah

Sudan: Al-Bashir zai fuskancin ICC bisa zargin kashe Bayin Allah
Omar Al-Bashir mai shekara 76 a Duniya zai hallara gaban ICC
Asali: UGC

“Mun yarda cewa duk wanda ake nema a kotu zai bayyana a gaban ICC. Ina fadan wannan da babbar murya.” Inji Eltaish.

Omar Al-Bashir wanda ya yi watsi da ikon kotun ICC a lokacin da ya ke kan mulki, ya bar kujerar shugaban kasa a Afrilun 2019.

Mahukuntan ICC su na bukatar a gurfanar da Omar Al-Bashir game da kisan da aka yi a Darfur, don haka ake nemansa a kotu.

Majalisar dinkin Duniya ta bayyana cewa bayan kisan gillar da gwamnatin Al-Bashir ta yi, ya daurewa wasu Sojoji gindi.

Gwamnatin Al-Bashir ta kafa wasu Sojoji da ake kira Janjaweed. Akalla mutane miliyan 2.5 su ka mutu a dalilin yakin da aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel