Kungiyar dattawan arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan rikicin Ganduje da Sarkin Kano

Kungiyar dattawan arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan rikicin Ganduje da Sarkin Kano

- Kungiyar dattawan arewa ta yi watsi da ikirarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa bai da hurumin sanya baki a rikicin da ke afkuwa tsakanin Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

- Dattawan sun ce a matsayin Buhari na jagoran al’umma, ba daidai bane ya ware kansa a gefe a lokacin da wani abu da ka iya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron wani yankin kasar ya kunno kai

- A cewar kungiyar aikata hakan ba zai zama yiwa kundin tsarin mulkin kasar shisshigi ba

Kungiyar dattawan arewa ta yi watsi da ikirarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa bai da hurumin sanya baki a rikicin da ke afkuwa tsakanin Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II saboda kundin tsarin mulkin kasar ya yi masa iyaka.

Kungiyar dattawan arewar ta ce a matsayin Buhari na jagoran al’umma, ba daidai bane ya ware kansa a gefe a lokacin da wani abu da ka iya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron wani yankin kasar ya kunno kai.

Kungiyar dattawan arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan rikicin Ganduje da Sarkin Kano
Kungiyar dattawan arewa ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan rikicin Ganduje da Sarkin Kano
Asali: Twitter

A cewar kungiyar aikata hakan ba zai zama yiwa kundin tsarin mulkin kasar shisshigi ba.

Sai dai kuma a martanin Shugaban kasar, wanda hadiminsa a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce ya san iyakarsa a matsayinsa na wanda aka zaba kan tafarkin damokradiyya.]

"Idan magana na a gaban kotu ko majalisa, Shugaban kasa Buhari bai da hurumin sanya baki, saboda idan ya aikata hakan toh lallai ya karya doka."

"Yana ganin gwamnatin Kano ita za ta magance duk wata matsala da ta taso da ke cikin huruminta," in ji Garba Shehu.

Amma dattawan na arewa na ganin akwai abubuwa da dama da shugaba zai yi ba sai kundin mulki ya ce ya yi wanda ba zai sa ya karya kundin tsarin mulkin ba.

A cewar Dr Hakeem Baba Ahmed, "bai dacewa a ce kana babba kuma ka ga ana rikici ka ki sa baki ba. Yana iya sa baki a rikicin Kano kuma akwai inda za a saurare shi a warware rikicin."

KU KARANTA KUMA: Asibitocinmu sun koma wajen ajiye gawa shiyasa Buhari ya ke zuwa kasar waje

"Amma kasa ido ka ce ba ruwanka, kuma kana matsayin shugaba akwai hakki," in ji shi.

Ya kuma ce sun yi mamakin yadda shugaban ya nada wani kwamiti na daban duk cewa su suka fara zuwa Kano a matsayin dattawan arewa da nufin sasanta rikicin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel