Yawan yaran da ba su karatun boko a Arewa ya na damun Aisha Buhari

Yawan yaran da ba su karatun boko a Arewa ya na damun Aisha Buhari

Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ce yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Yankin Arewacin Najeriya ya na da ban takaici.

Aisha Buhari ta yi wannan bayani ne wajen kaddamar da wani shiri da kungiyarta watau Future Assured ta kawo domin bunkasa ilmi da koya sana’a Najeriya.

Mai dakin shugaban Najeriyar ta kaddamar da wannan shiri ne a jihar Adamawa, inda za a samu kananan yara 750 da za a koyawa sana’a da kuma ba su ilmi.

Uwargidar shugaban kasa Buhari ta bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa game da wannan hali da ake ciki a Arewacin kasar.

“Mafi tada hankalin abin da ke faruwa shi ne a jihohin Arewa inda rikici da talauci su ke kara jefa mutane cikin matsala game da rashin isassun kayan karatu.”

KU KARANTA: Turai Yaradua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar Shugaban kasa

Yawan yaran da ba su karatun boko a Arewa ya na damun Aisha Buhari
Aisha Buhari ta ce an yi watsi da ilmin mata a Najeriya
Asali: Facebook

Hajiya Buhari ta ke cewa ana fama da rashin kayan aiki da wuraren daukar karatu, da kuma rashin isassun kwararrun Malaman, ban da matsalar albashi mai tsoka.

Abba Tahir ne wanda ya wakilci Uwargidar Najeriyar a wajen kaddamar da wannan shiri da dinbin jama’a za su amfana da wannan kungiya mai zaman kanta.

Dr. Abba Tahir shi ne mataimakin shugaban jami’ar Amurkan nan AUN, da ke Yola. A jawabinsa a madadin Buhari, ya yi kira da a dage wajen kai yara makaranta.

“Dole mu fahimci cewa sha’anin cigaba da su na tafiya ne da ilmi. Sai mun koma mun gano ainihin silar matsalar ilmi, tattalin arziki, aikin gona da sauransu.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel