Majalisa ta bukaci Shugaban Jam’ar ABU, Ibrahim Garba, ya tafi hutu tun a Maris

Majalisa ta bukaci Shugaban Jam’ar ABU, Ibrahim Garba, ya tafi hutu tun a Maris

Rigima ta barkowa jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya bayan da majalisar da ke kula da gudanarwa na jami’ar ta bukaci shugabanta watau Ibrahim Garba, ya tattara ya tafi hutu.

Wa’adin Farfesa Ibrahim Garba zai kare ne a Ranar 30 ga Watan Afrilun 2020, sai dai majalisar da ke kula da jami’ar ta aika masa takarda cewa ya tafu hutu tun a Watan Maris.

Farfesa Garba ya nuna cewa babu inda zai je, zai tsaya har sai ya ga karshen wa’adinsa, ya kuma mikawa sabon shugaban jami’ar ragamar mulki kafin ya bar ofis a farkon Mayu.

Magatakardar majalisar kuma Akawun jami’ar ABU, Malam A. A Kundila, shi ne wanda ya sa hannu a Ranar Juma’a a wannan takarda da ta fito daga karkashin Adamu Fika.

“A karshen zamanmu na gaggawa na 190, mun cin ma matsayar cewa mu bada umarni ka tafi hutun aiki daga Ranar 1 ga Watan Maris, Ka mika mulki ga Farfesa D.A Ameh.”

KU KARANTA: Shugabanni su na bukatar a sa su a cikin addu'o'i - Sultan

Majalisa ta bukaci Shugaban Jam’ar ABU, Ibrahim Garba, ya tafi hutu
Ana samun sa-in-sa tsakanin Adamu Fika da Ibrahim Garba a ABU
Asali: UGC

“Har zuwa lokacin da sabon shugaban jami’a zai shiga ofis a Ranar 1 ga Watan Mayu. Bayan haka kuma za ayi bincike game da ma’aikatan da aka dauka daga Oktoba zuwa yau.”

Malam Adamu Fika (Wazirin Fika) ya sanar da Ministan ilmi, Adamu Adamu, hukumar NUC, Sufetan ‘Yan Sanda, Darektan DSS da wasu hukumomin kasar game da matakin.

Shugaban kungiyar tsofaffin Daliban jami’ar ABU Zariya, Farfesa Ahmed Mora, ya aikawa majalisar takarda, ya na mai sanar da ita cewa babu inda doka ta ce a tura VC hutu.

Ibrahim Garba ya bayyana cewa ba zai je ko ina ba kamar yadda ake bukatarsa. Sannan kuma ya ce a ka’ida ko da ba ya nan, ba Farfesa Ameh ba ne zai rike jami’ar na rikon-kwarya.

A jami’a mataimakin shugaba (DVC) mai kula da harkar gudanarwa shi ne gaba da wanda ke kula da sha’anin karatu kamar yadda Farfesa Rabiu Magaji ya shaidawa Daily Trust.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel