Sanatan Neja ya koka kan sabbin hare-haren yan bindiga a jahar

Sanatan Neja ya koka kan sabbin hare-haren yan bindiga a jahar

Sanata mai wakiltan yankin Neja ta gabas, Mohammed Sani Musa, ya koka kan sabbin hare-haren yan bindiga a kan wasu garuruwa a jahar Neja.

Ya yi korafin cewa ana kaiwa yankinsa mummunan hare-hare na rashin tausayi.

Ya bayyana cewa sabbin hare-haren na zuwa ne bayan mutane sun fara dawowa hayyacinsu sakamakon alkawarin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na shiga lamarin.

A ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairu ne yan bindiga suka kai hari Gurmana da garuruwa a karamar hukumar Shiroro, garuruwan da ke kusa da Beni a karamar hukumar Munya, Adunu a karamar hukumar Paikoro da Tufa a karamar hukumar Gurara na jahar Neja.

Musa, wanda ya yi watsi da sabbin hare-haren ya bayyana su a matsayin rashin imani.

"Na samu labarin hare-haren safiyar Asabar daga al’umman garuruwan wadanda suka shad a kyar.

“Wannan abun bakin ciki ne. A daidai lokacin da muke tunanin hare-haren yan bindiga ya zo karshe tunda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga lamarin, sai ga wasu mummunan hare-hare da aka kai kan bayin Allah da basu jib a basu gani ba.

"Zuciyana ya yi nauyi, kuma na kasa yarda cewa mutane za su iya kasancewa da rashin tsoron Allah har ya kai ga rayukan jama’a ya zama ba komai ba a wajensu. Na samu rahoton abun bakin cikin da kuma hare-haren rashin imani da aka kai kan mutane na a safiyan nan.

“A bisa ga bayanin da na samu, yan bindiga sanye da bakaken kaya da rufaffen fuskoki sun kai mamaya garin Gurmana da wasu garuruwa sannan suka fara harbi ba kakkautawa. A cikin haka mutane biyu sun mutu yayinda hudu ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.”

KU KARANTA KUMA: Hare-haren yan bindiga: Shinkafi ya nemi a kama Yari a wata wasika zuwa ga IGP, DSS da sauransu

Dan majalisar, yayinda yake yaba ma jami’an tsaro a sabon kokarin da suke yin a magance rashin tsaro a jihar, ya bukaci da kada su yi kasa a gwiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel