PRP ta shirya doke APC, PDP a zaben 2023 – inji Falalu Bello

PRP ta shirya doke APC, PDP a zaben 2023 – inji Falalu Bello

Jam’iyyar adawar nan ta PRP ta bayyana shirinta na doke APC da PDP daga kan mulki a babbam zabe mai zuwa da za ayi a Najeriya a shekarar 2023.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Alhaji Falau Bello, shi ne ya bayyana shirin jam’iyyar na karbe mulki daga hannun ‘Yan siyasar APC da kuma PDP.

Falalu Bello ya nuna cewa a halin yanzu PRP ta dawo da karfinta, ta kuma shiryawa zaben da za ayi nan gaba. Lokacin tashi kurum ake jira inji Bello.

Alhaji Bello ya yi wannan bayani ne a Garin Kaduna a cikin makon nan, a wajen taron majalisun NEC da NWC da kuma BOT na Amintattun jam’iyyar.

“Ina so in yi amfani da wannan dama in tabbatarwa Abokan aiki na cewa duk tangal-tangal din da PRP ta shiga a baya, ta zo karshe.” Inji Falalu Bello.

KU KARANTA: PDP ta na so a dawowa Gwamna Ihedioha kujerarsa bayan hukuncin kotun koli

PRP ta shirya doke APC, PDP a zaben 2023 – inji Falalu Bello
Alhaji Falalu Bello ya ce sun babbako da Jam'iyyar PRP
Asali: Twitter

Shugaban jam’iyyar ya kuma ce: “Yanzu jam’iyyar mu ta PRP ta dawo kan hanya, ta dawo da sabon rai, kuma lokaci kurum ta ke jira domin ta mike.”

“Matakin da INEC kanta ta dauka game da jam’iyyar, wani abu daya ne da ke nuna cewa jirgin PRP ya samun karfin kama tafiyar da babu rana tsayawa.”

A yunkurin jawo jama’a, jam’iyyar ta yi kira cewa: “Wadanda su ke waje a yanzu, su shigo cikin tafiyar. Daga yanzu kuma babu wanda zai iya tsaida mu.”

PRP ta shirya wannan zama da ta yi ne domin ta duba rahoton da wasu kwamitocinta su ka yi game da zaben 2019, domin duba inda za ta sa kai a 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan labari. Kafin nan dama kun ji cewa hukumar iNEC ta soke rajistar jam’iyyun siyasa 74. PRP ta na cikin wadanda aka bari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel