‘Ya ‘yan PDP ne su ka koma aka kafa Jam’iyyar APC da su inji Sule Lamido
Alhaji Sule Lamido, wanda ya na cikin ‘Yan ga-ni-kashe-nin jam’iyyar adawa a yau ta PDP tun fil azal, ya zanta da Jaridar Daily Trust a cikin ‘yan kwanakin nan.
Sule Lamido ya nuna cewa bai ga abin yi wa APC adawa ba, domin da gumin PDP aka kafa ta.
“APC gwamnati ce da aka kirkira da PDP domin idan ka cire tsofaffin ‘Yan PDP babu yadda za ayi APC ta kai ga kafa gwamnati. Don haka rabin gwamnatin kusan ta mu ce.”
A game da komawa APC ya ce: “Na ji dadin yi mani wani tayi da ka yi a makare. Ana yin adawa ne ga jam’iyyar da ta ke da manufa tsayayya, ta ke da tsare-tsare da akidunta.”
“Duk wadanda ke cikin gwamnatin APC mai mulki, sun taba yin PDP. Mafi yawan Ministocinsu ‘Yan PDP ne a baya, idan ka cire Tinubu, kaf ‘Yan APC daga PDP su ka fito.”
Sule Lamido ya ce abin da ya ke so a zaben 2023, shi ne ‘Yan Najeriya su dauki darasi. Fitaccen Babban ‘Dan siyasar ya bayyana cewa faduwa zabe a 2015 bai dada sa da kasa ba.
KU KARANTA: Cancanta za ta yi aiki a 2023 bayan inda mutum ya fito ba - Sule
“Buhari ya yi duk wani irin gantali da bala-guron da wadanda su ka bar PDP su ka yi. Ya tafi APP ya karbe ta daga hannun wadanda su ka kafa ta; Okorocha da su Lema Jibrin.”
“Ya tafi APP ne kawai don ya samu tikitin takarar shugaban kasa. Daga nan ya sheka zuwa ANPP, sai kuma ya koma ya kafa jam’iyyarsa ta kansa watau CPC, a nan ma ya gaza.”
Daga nan sai ya dawo ya hada-kai da wasy daga cikin PDP da wasu jam’iyyun aka kafa APC. Inji Sule Lamido. A haka ne dai Buhari ya iya dace ya lashe zaben shugaban kasa a 2015.
Sule ya ce: “Na fadawa Abokai na na APC, ko na bi ku, hankali na ba zai kwanta ba, domin ni tsohon ‘Dan PRP ne, mun san daraja a siyasa. Akwai abin kunyan da ba zan iya ba.”
“Ba zan iya kunyata tarihi na ba. Ko da radadin talauci zai sa in fara tangadi ina magagi, da zarar na yi tunanin zan koma APC, zan farka, rai na zai fada mani cewa ba da kai ba."
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng