Ngozi Okonjo-Iweala ta shiga cikin shugabannin wata tsangaya a Havard

Ngozi Okonjo-Iweala ta shiga cikin shugabannin wata tsangaya a Havard

Mun samu labari cewa tsohuwar Ministar kudin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta shiga cikin shugabannin tsangayar John F Kennedy a jami’ar Harvard.

Kamar yadda labari ya zo mana, Ngozi Okonjo-Iweala ta na cikin idon sanin wannan tsangaya da aka kafa domin karantar da ilmin sha’anin gwamnati a jami’ar.

Wannan Jami’a ta Harvard ta na cikin manyan makarantun jami’o’in da ake da su a Amurka da kuma Duniya gaba daya kamar yadda alkaluma su ka nuna.

Darektan yada labarai da hulda da jama’a na tsangayar John F Kennedy mai suna James F Smith ne ya bada wannan sanarwa a cikin ‘yan kwanakin bayan nan.

Kafin yanzu tsohon shugaban kasar Columbia, Juan Manuel Santos, ya rike wannan matsayi. Tarja Halonen wanda ya yi mulki a Finland ya taba hawa kujerar.

KU KARANTA: Najeriya ta fi ko ina zaman lafiya - Ministan Gwamnati

Ngozi Okonjo-Iweala ta shiga cikin shugabannin wata tsangaya a Havard
Okonjo-Iweala ta zama idon Duniyar wata tsangaya a Harvard
Asali: UGC

Haka zalika kafin tsohuwar Ministar ta Najeriya, tsohon shugaban kasa Felipe Calderon ne Mexico ya rike wannan mukami, haka kuma Ban Ki Moon na majalisar UN.

Shugaban wannan tsangaya ta jami’ar, Douglas Elmendorf, ya nuna cewa Okonjo-Iweala za ta taimaka masu da tarin kwarewarta da sanin aiki da hangen nesa.

Douglas Elmendorf ya na ganin Dr. Okonjo-Iweala za ta magance kalubalen da ake fama da su wajen kawo cigaba a Yankin Afrika da sauran bangarorin Duniya.

‘Yan Najeriya sun fito su na taya tsohuwar Jami’ar gwamnatin kasar murnar samun wannan matsayi. A baya kamfanin Tuwita ta zabe ta cikin manyan Darektocinta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel