Majalisa za ta hana Ma’aikatu kudinsu, ta kuma sa a cafke Gwamnan CBN Emefiele

Majalisa za ta hana Ma’aikatu kudinsu, ta kuma sa a cafke Gwamnan CBN Emefiele

Majalisar Wakilai ta fara barazanar bada umarnin a cafko shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatu na tarayya a dalilin kin amsa gayyatar da aka yi masu a wani bincike da ake yi.

‘Yan majalisar sun gayyaci wasu shugabannin MDA sun hallara gabansu a sakamakon wani bincike da ake yi a kasar. Wasu shugabannin sun yi watsi da wannan gayyata da aka yi masu.

A dalilin rashin bada hadin-kai, Majalisar ta bakin Kakakinta, Femi Gbajabiamila, da shugaban kwamitin da ke kula da kudin al’umma, Wole Oke, su ka yi wa hukumomin wannan barazana.

Manyan ‘Yan majalisar sun yi wannan magana ne a Ranar Litinin, inda su k ace su na binciken hukumomi da ma’aikatun da su ka ki dawo da rarar kudin da ya rage masu daga 2014 zuwa 2018.

Mataimakin masu rinjaye, Peter Akpatason, shi ne ya wakilci Femi Gbajabiamila a zaman. Akpatason ya ce gwamnan CBN, da babban Mai binciken kudi a kasar su na cikin masu laifi.

KU KARANTA: Buhari: An kafa kwamiti domin duba rashin tsaro a Najeriya

Majalisa za ta hana Ma’aikatu kudinsu, ta kuma sa a cafke Gwamnan CBN Emefiele
Gwamnan CBN ya na cikin wadanda su ka yi watsi da kiran Majalisa
Asali: UGC

“Ba a wasa da aikin kwamitin kudi a duk majalisun Duniya saboda rawar da su ke takawa. Watsi da kiran wannan kwamiti a irin wannan lokaci ya sabawa doka, kuma za a dauki mataki."

A cewar 'Dan majalisar tarayyar, “Majalisa ba ta ji dadin ganin yadda wasu ma’aikatun gwamnati irinsu CBN da ofishin Mai binciken kudi, ba su halarci wannan zama na yau (Litinin) ba."

“An ba ni alkaluman Ma’aikatun da su ka ki maidawa gwamnati rarar kudinsu a shekarun nan. Sai mun jira shugaban kasa ya shigo cikin lamarin, ya sa baki bayan nauyin da ke kan MDA?”

Majalisar ta yi barazanar bada umarni a kama wadanda su ka sabawa doka, tare da buga sunayen hukumomi da ma’aikatun da su ka saba dokan a jaridu kamar yadda mu ka samu labari jiya.

Hon. Wole Oke ya kuma nuna cewa za su iya sa a dakatar da kason kudin wadannan ma’aikatu daga cikin kasafin kudin kasa. Oke ya ke cewa majalisa ba za ta cigaba da karbar uzuri ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng