Ka taba gidajen mutane, mu shirya maka maka zanga-zanga – Yari ga Matawalle
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulazeez Yari, ya fito ya na mai tabbatarwa Magoya bayan APC cewa babu wanda zai rusa masu gidajensu.
Alhaji Abdulazeez Yari ya fadawa Masoyan jam’iyyar APC cewa gwamnatin jihar Zamfara ta Bello Matawalle ba za ta taba gidan kowa ba.
Idan ba ku manta ba kwanaki gwamnatin jihar ta ruguza ofishin jam’iyyar APC a Garin Muradun, kuma ta ce za ta kauda wasu gidajen jama’a.
Abdulazeez Yari wanda ya yi mulki tsakanin 2011 zuwa 2019 ya fadawa wadansu ‘Ya ‘yan APC cewa gwamnati ba za ta sake rusa wani gini ba.
Yari ya yi wannan bayani ne a lokacin da wasu ‘Yan APC su ka kai masa ziyara a gidansa da ke cikin Garin Talata-Mafara a jiya Ranar Lahadi.
KU KARANTA: Sabon Gwamnan Imo ya fallasa masu neman yi wa Buhari juyin mulki

Asali: Twitter
An rahoto tsohon gwamnan ya na cewa: “Bari in yi kira ga Gwamna Matawalle da ya daina rusa gidajen Magoya bayan APC a jihar Zamfara.”
A sakamakon haka, Abdulazeez Yari ya cigaba da cewa: “Idan ba haka ba, duk abin da ya faru a jiharmu shi (Bello Matawalle) shi zai dauki alhaki.”
Tsohon shugaban gwamnonin Najeriyar ya gargadi gwamnatin PDP da ke ci a jihar da cewa idan ba ta dauki shawararsa ba, sai yabawa aya zaki.
“Ni da kai na zan jagoranci zanga-zangar da za ayi wa gwamnati Matawalle idan ya taba wani daga cikin gidajen ‘Ya ‘yan jam’iyyarmu (APC)."
“Idan kuma ya dauka cewa ba’a na ke yi, ya jarraba hakan, ya ga abin da zai faru.” Inji Yari.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng