Yan bindiga sun yi garkuwa da Mata da Miji a babban birnin tarayya Abuja

Yan bindiga sun yi garkuwa da Mata da Miji a babban birnin tarayya Abuja

Wasu gungun miyagu yan bindiga dadi sun yi garkuwa da wani mutumi mai suna Abdullahi Otto tare da matarsa mai dauke da juna biyu, Maimuna Abdullahi daga gidansu dake babban birnin tarayya Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ranar Asabar, 1 ga watan Feburairu a gidan ma’auratan dake unguwar Kekeshi dake cikin karamar hukumar Abaji na Abuja, kamar yadda wani dan uwan Abdullahi daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar.

KU KARANTA: Bayan watanni 10 a hannu, dan bautan kasa kirista ya bayyana dalilin da yasa yake son cigaba da zama tare da Boko Haram

Majiyar ta kara da cewa dan uwan Abdullahi yace da misalin karfe 10:34 na daren Asabar ne yan bindigan da adadinsu ke da yawa suka kutsa kai gidan ma’auratan dauke da muggan makamai suna harbe harbe a sama.

Shigarsu ke da wuya suka dauke ma’auratan ba tare da wani bata lokaci ba, sa’annan harbe harben da suka dinga yi ya sanya makwabta kowa ya yi ta kansa, babu wanda ya yi ihu balle ya kai musu agaji.

Daga bisani yan bindigan sun tuntubi iyalan ma’auratan, inda suka nemi a biyasu naira miliyan 3 a matsayin kudin fansa kafin su sake su, amma abin da iyalan suka iya hadawa kawai shi ne N600,000, tayin da miyagun suka yi fatali da shi.

Ko da majiyarmu ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar Yansandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja, DSP Anjuguri Manzah game da lamarin, sai yace ba shi da masaniya, amma zai duba.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sanye da kayan Sojoji da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun bude ma wasu babbar motar Luxurious wuta a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja inda suka ji ma mutane hudu rauni.

Wannan lamari ya faru ne a gab da kauyen Gada-Biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu, inda yan bindigan suka bude ma motar kamfanin Chisco wuta mai lamba AGL 11 XL.

Direban babbar motar mai suna Madu Francis ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:47 na yamma a lokacin da yake gangarawa Gada-Biyu, kwatsam sai ganin wasu mutane sanye da kakin Sojojo sun fito daga cikin daji sun bude musu wuta da bindigu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel