Buhari: Ka da ka kama layin irin mulkin Adolf Hitler – Inji Shehu Sani

Buhari: Ka da ka kama layin irin mulkin Adolf Hitler – Inji Shehu Sani

Fitaccen ‘Dan gwagwarmayan nan, Sanata Shehu Sani, ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta guji komawa bakin mulki.

Shehu Sani ya yi wannan kira ne bayan ya sha damka a hannun hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, a Watan jiya.

Sani a wani jawabi da ya fitar a karshen makon nan, ya nemi kowane bangare na gwamnati a Najeriya ya tsaya a huruminsa ba tare da wuce iyaka ba.

Shehu Sani ya ce:

“A ka’idar mulkin farar hula, ya zama dole ga kowace ma’aikatar gwamnati ta yi aiki da tsarin mulki da doka, sai dai kuma idan ta koma kama-karya.”

KU KARANTA: Lokacin da Shehu Sani ya bankado da sirrin 'Yan Majalisa

Buhari: Ka da ka kama layin irin mulkin Adolf Hitler – Inji Shehu Sani
Sani ya kamanta Gwamnatin Tarayya da ta Adolf Hitler
Asali: Twitter

“Littafin Stalin, ka’idojojin Hitler da kuma kundin tafarkin Mussolini, ba su ya kamata gwamnati ta yi amfani da su wajen yaki da rashin gaskiya ba.”

Tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa bai kamata hukumomin da ke yaki da Barayi su kauce hanya wajen kokarin gyara kasa ba.

Tsohon ‘Dan majalisar ya yi wannan jawabi ne bayan ya shafe kwanaki 30 a hannun EFCC. Da fitowarsa ya godewa Alkalan kotu da su ka bada belinsa.

Sani ya kuma jinjinawa kungiyoyin kare hakkin Bil Adama irinsu Amnesty International, SERAP, HURIWA da su ka tsaya masa lokacin da ya ke tsare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel