Trump: Najeriya da wasu Kasashen Duniya sun rasa damar zuwa Amurka su tare

Trump: Najeriya da wasu Kasashen Duniya sun rasa damar zuwa Amurka su tare

Gwamnatin Donald Trump ta bada sanarwar cewa wasu kasashe sun shiga cikin jeringiyar wadanda ta makawa takunkumin samun takardun shiga na bizan Amurka.

Najeriya ta na cikin wadannan kasashe da su ka gaza cika sharudan tsaron Amurka. Sauran kasashen su ne: Eritrea, Sudan, Tanzania, Kyrgyzstan da kuma Myanmar.

A cikin kasashe nan babu wanda wannan doka za ta taba irin Najeriya. Daily Trust ta ce a bara, ‘Yan Najeriya da su ka je Amurka sun haura yawan Mazauna kasashen biyar.

Kawo yanzu wasu su na daukar cewa wannan mataki da aka dauka ya na nufin ‘Yan Najeriya ba za su sake iya shiga Amurka ba, Jaridar ta fayyace abin da dokar ta ke nufi.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta kafa wani kwamiti da zai duba wannan takunkumi. Hakan na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya fito ya nuna takaicinsa kan lamarin.

KU KARANTA: Coronavirus: 'Yan Najeriya da ke kasar Sin ba su son dawowa gida

1. Mutanen Najeriya ba za su samun bizar da za ta ba su damar zama a Amuka na din-din-din ba.

2. Wannan doka za ta fara aiki ne nan da makonni uku, a Ranar 21 ga Watan Fubrairun 2020.

3. Dokatarwar da aka y wa kasashen na wuce-gadi ne. Da zarar Najeriya da sauran kasashen sun cika sharudan tsaron Amurka, za a janye wannan takunkumi.

4. ‘Yan Najeriya za su samu takardun biza na shiga Amurka na takaitaccen lokaci. Hakan na nufin Mutanen wadannan kasashe za su iya zuwa Amurka domin fatauci ko kuma su ga Likita, da sauransu.

Wannan doka ba za ta yi aiki a kan Bayin Allah da za su shiga Amurka na wani ‘dan lokaci su fito ba, abin da aka hana shi ne a kyale mutanen kasashen su samu gindin zama.

Duk wani Mutumin Najeriya, da kasar Eritriya, Sudan, Tanzaniya, Kyrgyzstan da Myanmar ba zai samu takardun da za su ba shi damar zaman dirshen a cikin kasar Amurka ba.

A baya kun ji cewa shugabannin Majalisar kasar Amurka ba su goyon-bayan Donald Trump na hana Najeriya da sauran kasashe zama a kasar, don haka za su kawo sabon kudiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel