An kori shugaban 'sashe' a KADPOLY saboda neman daliba da lalata

An kori shugaban 'sashe' a KADPOLY saboda neman daliba da lalata

Hukumar kwalejin kimiyya dake Kaduna, watau KADPOLY, ta sallami tsohon shugaban sashen fasaha (Civil Engineering), Injiniya Danjuma Alhassan, bisa zarginsa da neman lalata wata dalibar makarantar.

A ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, 2020, mahukuntan kwalejin suka amince da bukatar a kori Alhassan daga bakin aiki yayin wani taro da suka gudanar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Samuel Y. Obochi, mataimakin rijistara mai kula da yada labarai da aiyuka na musamman.

Kazalika, hukumar kwalejin ta dakatar da wani shugaban 'sashe', da ba a bayyana sunansa ba, bayan samunsa da laifin karbar cin hanci daga hannun dalibai domin tsallakar da su jarrabawar da suka fadi.

An kori shugaban 'sashe' a KADPOLY saboda neman daliba da lalata
An kori shugaban 'sashe' a KADPOLY saboda neman daliba da lalata
Asali: UGC

An gano cewa lakcaran yana karbar kudi daga hannun dalibai tare da basu damar sauya takardar jarrabawa da zasu sake rubuta jarrabawar bayan sun fadi da aka kammala duba wa.

DUBA WANNAN: Kimanin mutane 20 sun mutu a 'turereniyar' karbar 'mai' na musamman a Coci

Yayin wata hirarsa da jaridar Daily Trust, sabon shugaban kwalejin, Idris Bugaje, ya bayyana cewa ya kirkiri wani sashe na musamman da aka yi wa lakabi da PTU (Policy and Transaparency Unit) domin zakulo batagari daga cikin ma'aikatan kwalejin da kuma bullo da tsare - tsare masu ma'ana da zasu inganta harkokin makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel