Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya

Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya

Uwar jam’iyyar PDP ta mika kukanta ga manyan kasashen duniya guda biyu, kasar Amurka da kasar Birtaniya, kan shari’ar hukuncin kotun koli daya kwace kujerar gwamnanta a jahar Imo, inda ta nemi kasashen biyu su agajeta.

Shugaban jam’iyyar APC, Cif Prince Uche Secondus da sauran shuwagabannin jam’iyyar ciki har da dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar, Peter Obi ne suka gudanar da zanga zangar lumana har zuwa ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Kunar bakin wake ya dawo a Maiduguri: Karamar yarinya ta kashe mutane 3 a Islamiyya

Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya
Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya
Asali: Facebook

PDP a karkashin jagororin zanga zangar ta bayyana ma kasashen biyu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC sun gaza matuka wajen magance matsalar tsaro data dabaibaye Najeriya, tare da kawo karshen kashe kashen mutane babu gaira babu dalili.

Haka zalika PDP ta yi kira ga kasashen biyu dasu tabbata an yi adalci a hukuncin kotun koli bayan ta sake komawa gaban kotun tana neman kotun ta sake duba shari’ar da ta yanke a baya daya kwace kujerar Gwamna Ihedioha na PDP ya baiwa Gwamna Uzodinma na APC.

PDP dai tana neman kotun koli ta sake gudanar da nazari da idon basira a kan wannan hukunci, tare da duba yiwuwar sake maido mata da kujerarta, wanda tun farko tace kotun ta yi kuskure wajen kwaceta.

A wani labarin kuma, rahotanni sun tabbatar da cewa matasa masu yi ma kasa hidima sun fara samun sabon alawus na naira dubu talatin da uku (N33,000) kamar yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki alkawari.

A cikin wannan makon ne shugaban hukumar NYSC, Shuaibu Ibrahim ya sanar da karin kudin alawus din, inda yace yana sa ran nan bada jimawa ba gwamnati za ta fara biyan kudin bayan samun amincewa daga shugaban kasa.

Sai ga shi kwatsam a ranar Alhamis yan bautan kasa sun fara samun sakon shigar kudi na bankuna dake tabbatar musu da sabon albashin, yan bautan kasa masu amfani da bankin Zenith ne suka fara samun kudin, yayin da sauran bankunan suka fara biya a ranar Juma’a, 31 ga watan Janairu.

Kafin wannan kari, yan bautan kasa suna amsan N19,000 ne a matsayin alawus dinsu na wata wata, shi ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya yi musu wannan karin a shekarar daya kara karancin albashi zuwa N19,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel