Yanzu-yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Hope Uzodinma, sabon gwamnan Imo (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Hope Uzodinma, sabon gwamnan Imo (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sabon gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban kasa, AsoVilla, Abuja a ranar Juma'a, 31 ga Junairu, 2020.

Hope Uzodinma ya samu rakiyar shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomole.

Yayinda Hope Uzodinma da Oshiomole ke wannan ziyara, shugabannin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP na gudanar da zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka da Ingila kan hukuncin kotun koli a zaben gwamnan jihar Imo.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

KU KARANTA: Sanusi vs Ganduje: An kaddamar da sabon bincike kan masarautar Kano

Bayan haka, Kakakin Majalisar jihar Imo, Chiji Collins ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).

Hakazalika yan majalisar dokokin jihar Imo akalla 19 sun koma APC.

Wadanda suka sauya shekar tare da kakakin sun hada da: Dominic Ezerioha mai wakiltar Oru ta yamma, Chigozie Nwaneri mai wakiltar Oru ta gabas, Kanayo Onyemaechi mai wakiltar Owerri ta yamma, Kennedy Ibe mai wakiltar Obowo da Onyemaechi Njoku mai wakiltar Ihitte/Uboma.

Eddy Obinna mai wakiltar Aboh Mbaise ya koma APC duk da kuwa karamar hukumarsu daya da Emeka Ihedioha.

Yanzu-yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Hope Uzodinma, sabon gwamnan Imo (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Hope Uzodinma, sabon gwamnan Imo (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel