Duk masu kira ga shugaban kasa ya yi murabus wawaye ne – fadar shugaban kasa

Duk masu kira ga shugaban kasa ya yi murabus wawaye ne – fadar shugaban kasa

Fadar shugaban shugaban gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, ta mayar da martani ga masu kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mukaminsa, inda tace hakan wawanci ne ba wani abu ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu inda yace wawanci ne Sanata Eyinna Abaribe ya nemi Buhari ya sauka daga mulki.

KU KARANTA: Rai ba a bakin komi ba: Yan fashi da makami sun bindige matashi dan bautan kasa

Daily Trust ta ruwaito Garba yana cewa wannan ra’ayi ne na wani mutum daya kacal, ba ra’ayin yan Najeriya ba, don kuwa shugaban kasa na aiki tukuru wajen tabbatar da tsaron Najeriya da yan Najeriya daga hare haren yan ta’adda da suka mamaye yankin Afirka.

“A kan me shugaban kasa Buhari zai sauka? Kawai saboda wani yana ganin ya kamata shugaba Buhari ya sauka, sai kawai ya sauka? Wannan ba ra’ayin yan Najeriya bane, wannan ra’ayi ne na wani mutumi daya saba sambatu.

“Idan har ya kamata shugaba kamar shugaban kasa Buhari ya yi murabus, akwai miliyoyin yan Najeriya da dama da suka fi cancanta su yi murabus, daga ciki har da Sanata Abaribe wanda ya bude kofar da wani mai ci amanar kasa ya bi ya tsere.” Inji shi.

Garba yace Sanata Abaribe ne ya tsaya ma shugaban kungiyar ta’addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu har ya tsere daga Najeriya, kuma har yanzu Sanatan ya kasa gabatar da Kanu gaban kotu don ya fuskanci hukunci, don haka mutum kamarsa ba shi da bakin da zai ce wani baya bin doka.

Garba ya cigaba da watsa maganganu masu zafi ga Abaribe, inda ya kara da cewa: “Kamata yayi Abaribe ya maye gurbin Kanu a gidan yari tund dai ya gaza wajen gabatar da shi gaban kotu. Jam’iyyar Abaribe ce ta lalata kasar nan har ta kusan durkushewa gaba daya a 2015, lokacin da Buhari ya amshe ta, kuma yake gyaranta.”

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai dai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel