Yanzu Yanzu: Obaseki ya sha alwashin gasa wa Oshiomhole aya a hannu idan ya cigaba da hargitsa al’amuran APC a Edo
- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya sha alwashin gasa wa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole aya a hannu idan har ya cigaba da hargitsa ayyukan APC reshen jahar
- Obaseki ya ce Oshiomhole ba zai taba lamuntan abunda shi yake lamunta na rashin da’a ba a lokacin da ya ke a matsayin gwamna
- Ya ce zai nuna wa shugaban APC din na kasa cewa shine gwamnan jahar Edo
Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya sha alwashin gasa wa tsohon gwamnan jihar kuma Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Comrade Adams Oshiomhole aya a hannu idan har ya cigaba da hargitsa ayyuka a jihar da kuma APC reshen Edo.
Gwamna Obaseki ya ce Oshiomhole ba zai taba lamuntan abunda shi yake lamunta na rashin da’a ba a lokacin da ya ke a matsayin gwamna.
Obaseki wanda ya yi magana a lokacin da ya halarci taron shugabannin kananan hukumomi 18 na APC a jihar ya ce zai nunawa Oshiomhole cewa shine gwamnan jihar.
Gwamnan na Edo ya ce APC reshen jihar na danasanin daukaka Oshiomhole ba tare da ta san irin mutumin da yake ba.
Ya umurci shugabannin jam’iyyar da su gallaza wa duk mutane ko kungiya da ke gudanar da ayyukan da suka saba ma yarjejeniyar jam’iyya.
KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 12 da mutum zai bi don kiyaye kamuwa da zazzabin Lassa
Gwamna Obaseki ya bayyana cewa Oshiomhole ba shine ya gina APC ba domin babu tubalin jam’iyya a lokacin da ya zama gwamna.
A wani labari na aban, mun ji cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Comrade Adams Oshiomhole a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, ya ce kin cike gurbin Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai alamu ne da ya nuna cewa mambobin majalissar sun san cewa lallai Alhassan Doguwa zai sake dawowa majalisar.
Oshiomhole ya fai hakan ne a yayinda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sauran mambobin majalisar dokokin tarayya na APC don kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa na Asokoro da ke Abuja.
An sake zabar Doguwa a zaben da aka sake gudanarwa a ranar Asabar da ya gabata domin cigaba da wakiltan al’umman mazabar Doguwa/Tudunwada a jihar Kano.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng