Yanzu lokaci ya yi da zan huta, in kuma fara tanadin gaba – Inji Hon. Jibrin

Yanzu lokaci ya yi da zan huta, in kuma fara tanadin gaba – Inji Hon. Jibrin

Kwanaki kadan bayan hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben majalisar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana inda ya sa gaba.

Yunkurin Abdulmumin Jibrin na sake komawa majalisar wakilan tarayya a wani karon bai yiwu ba bana, bayan rashin nasararsa a zaben makon jiya.

Hon. Jibrin ya wallafa wani bidiyonsa a kan lilo ya na kokarin lazumi. ‘Dan siyasar ya na sanye da fararen kaya da ya saba, amma bai ce komai ba.

Tsohon ‘Dan majalisar ya yi wani jawabi a rubuce a shafinsa na Tuwita da ya fito da wannan bidiyo ya na nuna cewa ya fara shirin tarar gaba.

“Bayan gwagwarmaya, lokaci ya yi da za mu ja numfashi, mu huta, mu kuma shakata da rashin dar-dar dinnan bayan shekaru goma 15 ana fafatawa.”

KU KARANTA: PDP ta rankwala Jibrin da kasa a zaben Majalisar Kiru da Bebeji

Tsohon ‘Dan majalisar wakilan ya kara da cewa: “An samu damar bibiyar baya, mu yi tunani, mu dauko kayan aiki, mu fara shiryawa tanadin gobe.”

Dr. Jibrin ya fara zuwa majalisa ne a 2011 a karkashin PDP. Daga baya kuma ya na cikin wadanda su ka bi tafiyar APC, har ya kuma zarce a zaben 2015.

‘Dan majalisar ya samu kansa cikin matsala a 2019, inda ya tsallake rijiya da kyar a zaben da aka yi. A cewarsa wannan ne zaben da ya fi ba shi wahala.

Daga baya kotu ta ruguza zaben na shi, ta bada umarni a shirya sabon zabe. Ana zargin cewa wasu kalamai da ya taba yi su ka sa APC ta juya masa baya.

‘Dan majalisar ya taya Ali Datti Yako nasarar lashe zaben, amma ya yi ikirarin cewa magudi aka yi masa, kuma duk da haka ba zai shigar da kara a kotu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel