INEC ta kashe zabukan karashen da su ka gudana a A/Ibom da C/Rivers

INEC ta kashe zabukan karashen da su ka gudana a A/Ibom da C/Rivers

Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, ta ce ta ruguza sababbin zabukan da ta shirya a wasu bangarorin kasar nan a cikin karshen makon da ya gabata.

INEC ta bayyana cewa ta kashe zabukan da aka yi a wasu rumfunan zabe a zabukan karashen da aka shirya a Garuruwan da ke Kuros Riba da kuma Akwa Ibom.

A wani jawabi da hukumar ta aikawa Manema labarai a Ranar Talata, 28 ga Watan Junairu, aka bayyana wannan mataki da aka dauka kwanaki da yin zaben.

Kwamishinan wayar da kan jama’a da yada labarai na hukumar INEC, Festus Okoye, shi ne ya sa hannu a wannan jawabi da aka aikawa ‘Yan jarida a fadin kasar.

Okoye ya bayyana cewa hukumar INEC ta cin ma wannan matsaya ne a sakamakon sabawa dokokin zabe da aka rika yi a wadannan wurare da abin ya shafa.

Hukumar ta bayyana cewa wannan matsala ta shafi Mazabu hudu ne kacal daga cikin Mazabun da aka shirya danyen zabe a makon jiya, a nan kadai aka kashe zaben.

KU KARANTA: Kujerar Majalisa ta fadi daga hannun APC ta koma PDP a Sokoto

INEC ta gudanar da zabe ne a Mazabu 28 a sakamakon umarnin da kotu su ka bada na soke zabukan da aka gudanar a 2019 ko mutuwar wanda ke kan kujera.

Jawabin da INEC ta fitar ya na cewa: “A Garin Isa a jihar Sokoto, ta’adin ‘Yan daban siyasa ya hana hukuma ta tura mutane zuwa wasu rumfunan zabe a Yankin”

“Amma daga baya, an yi nasarar tura Jami’ai, su ka shirya zabe kalau kuma su ka bayyana sakamako.” Hukumar INEC ta bayyana wannan a shafin ta na Tuwita.

”A Mazabar jihar Ibi da ke Jihar Kuros Riba, an sace Jami’an zabe wanda wannan ya sa aka gaza yin aiki a rumfunan zabe takwas da ke yankin.” Inji Hukumar.

Jawabin na INEC ya ce a wurare da-dama, rikicin da aka samu bai yi kamari ba, don haka wannan bai yi tasirin da zai shafi sakamako da nasarar ‘Dan takara ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel