Lalong ya yi umurnin kama shugabannin wasu garuruwa cikin gaggawa yayinda yawan mutanen da suka mutu a harin Plateau ya kai 22
- Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau, a ranar Talata, 28 ga watan Janairu ya yi umurnin dukkanin shugabannin Fulani a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, Riyom da Barkin Ladi da ke jihar
- Hakan ya biyo bayan samun labarin yawan adadin mutane dda suka mutu a harin karshen mako wadanda suka kai 22
- Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan yan sanda, Isaac Akinmoyede a lokacin wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki, shugabannin Fulani da shugabannin garuruwa da na addini wanda ya gudana a gidan gwamnati a Jos
Gwamnan jihar Plateau kuma Shugaban gwamnonin Arewa, Simon Lalong a ranar Talata, 28 ga watan Janairu ya yi umurnin dukkanin shugabannin Fulani a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, Riyom da Barkin Ladi da ke jihar yayinda yawan mutanen da suka mutu a harin karshen mako ya tasar na 22.
Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan yan sanda, Isaac Akinmoyede a lokacin wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki, shugabannin Fulani da shugabannin garuruwa da na addini wanda ya gudana a gidan gwamnati a Jos.
Gwamnan wanda ya fusata da nuna bakin ciki a kan cigaba da kai hare-haren da kashe-kashe da yan bindiga ke kaiwa wasu kauyuka a Bokkos da Mangu, ya ce ba zai sake lamuntan haka ba.
“Ina magana ne a madadin jihar Plateau a matsayin shugaban tsaro, tunda ba a kama kowani mai laifi ba kuma har yanzu ana kashe mutane; a kama dukkanin Ardon Fulani da shugabannin garuruwan har sai an fito da wadanda suka aikata laifin.
“Bama tsoron wadannan yan ta’addan, babu wanda ya fi karfin gwamnati! Ta yaya za ku fada mani cewa ba a kama kowa ba, shin aljanu ne masu kisan? Allah zai Tina masu asiri kuma ba zan sake lamunta ba a jihar Plateau ya isa haka!”
Lalong wanda ya nuna bakin ciki da bacin rai a kan kashe-kashen, ya yi umurnin gaggawan kama Shugabannin Fulani da na garuruwan da suka halarci taron, sannan cewa a tsare su a hannun yan sanda har sai an fito da masu laifin.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta dawo sannan ta dage zamanta don jimamin mutuwar wani dan majalisar wakilai
Kwamishinan yan sandan ma ya nuna bakin ciki kan cewa wasu shugabanni na boye masu laifi a garuruwansu wadanda ke kaddamar da hare-hare da kashe-kashe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng