PDP: An soki Dave Umahi a kan nuna goyon bayansa ga Godwin Obaseki
Gwamna Dave Umahi bai jin dadin yadda abubuwa su ke masa tafiya a jam’iyyar PDP tun bayan da ya tofa albarkarsa ga Takwaransa, Godwin Obaseki, na jihar Edo.
Mai girma gwamna Godwin Obaseki ya na karkashin jam’iyyar APC mai mulki ne yayin da Dave Umahi ya ke mulkin jihar Ebonyi a karkashin jam’iyyyar adawa ta PDP.
Mista Godwin Obaseki ya na kan wa’adinsa na farko ne a mulki, kuma ya ce zai nemi tazarce a shekarar nan a tsakiyar rikicin da ya ke yi da shugaban jam’iyyar APC.
Albarkar da gwamnan na Ebonyi ya sa wa Godwin Obaseki ya jawo masa matsala daga wajen jam’iyyarsa, inda su ke ganin hakan na iya kawo masu matsala a zaben Edo.
PDP ta zargi gwamnan na ta da rashin da’a saboda nuna goyon baya ga Abokin gaba. A na ta bangaren, ta na ganin wannan aiki ya na iya jawowa ‘Dan takararta cikas.
KU KARANTA: Obaseki na APC zai zarce a kan karagar mulki - Umahi
Jaridar nan ta Premium Times ta rahoto Mista Dan Orbih ya na cewa goyon bayan da Umahi ya ba Obaseki ya kashewa wasu ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP karfin-gwiwa a Edo.
Shugaban jam’iyyar adawar na jihar Edo, Dan Orbih ya bayyana wannan ne a wata wasika da ya aika zuwa ga shugabannin jam’iyyar PDP da ke Garin Abuja kwanan nan.
Orbih ya roki shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya ja kunnen ‘Ya ‘yansa da ke fitowa su na nuna su na tare da gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar APC.
Haka zalika shugaban na PDP ya kuma zargi tsohuwar Sanatan jam’iyyar, Daisy Danjuma da yi wa Godwin Obaseki mubaya’a, har ta na cewa ba ta yi da-na-sanin yin haka ba.
Kwanakin baya ne gwamnan na Ebonyi ya tofawa Obaseki albarka lokacin da Betty Obaseki da wasu manyan jihar Edo su ka kawo masa ziyara a babban birnin Abakalilki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng