Buhari: Ramuwar gayya ba ta da wuri a al’ummar da ta tara jama'a daban-daban

Buhari: Ramuwar gayya ba ta da wuri a al’ummar da ta tara jama'a daban-daban

A Ranar Litinin aka ji shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na kokawa game da hare-haren da aka kai a cikin ‘yan kwanakin nan a Jihar Filato.

A farkon makon nan da ake ciki, Shugaban kasar ya bayyana cewa bai da ce jama’a su rika yin ramuwar gayya na kashe-kashen da aka yi masa ba.

A cewar Buhari, ramuwar ba ta da hurumi a cikin Kasa irin Najeriya wanda ta kunshi mutane masu ra’ayin addini daban da kuma banbancin kabila.

Muhammadu Buhari ya yi wannan magana ne a sakamakon harin da wasu ‘Yan bindiga su ka kai a jihar Filato wanda ya yi sanadiyyar ajalin mutum 13.

Shugaban na Najeriya ya tabbatarwa Jama’a cewa zai kawo karshen ta’addanci, satar dabobbi, garkuwa da mutane da sauran mugayen laifuffuka.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar wani Hakimi a Katsina

Buhari: Ramuwar gayya ba ta da wuri a al’ummar da ta tara jama'a daban-daban
Buhari ya na so Malamai da Shugabanni su rika fadakar da al’umma
Asali: UGC

A jawabinsa ya ce: “A jihar Filato, Wasu ‘Yan bindiga sun sake kai wani hari, su ka buda wuta, su ka kashe mutanen da ba su yi laifin komai ba.”

Buhari ta bakin Mai magana da yawun bakinsa watau Garba Shehu ya kara da cewa: “Ya kamata kowa ya yi Allah-wadai da wannan abin takaici”

Shehu ya bayyana cewa shugaban kasar ya tada Tawaga ta musamman domin ta yi wa mutane da gwamnatin Filato da wannan abu ya shafa ta’aziyya.

Shugaban kasar ta bakin Hadiminsa ya kuma yi kira ga jami’an tsaro su kara zage damtse, tare da rokon shugabanni da su rika jan hankalin Matasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel