Murnar nasarar APC: Jami'in NSCDC ya harbe dan takarar Sanata a Imo

Murnar nasarar APC: Jami'in NSCDC ya harbe dan takarar Sanata a Imo

An shiga halin rudani da firgici ranar Lahadi sakamakon harbe Ndubuisi Emenike, dan takarar kujerar sanatan jihar Imo ta arewa a karkashin jam'iyyar AA, da wani jami'in hukumar tsaron hukumar NSCDC ya yi.

Lamarin ya faru ne da misain karfe 5:00 na yamma a wurin bikin samun nasarar lashe zaben maye gurbin kujerar majalisar wakilai na mazabar Okigwe da APC ta yi.

A ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da 'yar takarar APC, Miriam Onuoha, a matsayin wacce ta samu nasarar lashe zaben maye gurbi da aka yi ranar Asabar, kuma a wurin bikin samun nasararta da ake yi a gidanta dake Umanachi, karamar hukumar Isiala Mbano, lamarin ya faru.

Jaridar Punch ta rawaito cewa jami'in NSCDC din da ya harbe dan takarar yana aiki ne tare da shi, hasali ma shine ya raka shi wurin bikin murnar da ake yi a gidan Onuoha.

Jami'in ya harbi maigidan nasa ne bisa kuskure yayin da yake harbin iska a wurin bikin, lamarin da ya kawo karshen bikin murnar da ake yi, kamar yadda wani shaidar gani da ido ya shaida wa jaridar Punch.

Murnar nasarar APC: Jami'in NSCDC ya harbe dan takarar Sanata a Imo
Jami'an NSCDC
Asali: Depositphotos

An garzaya da dan takarar sanatan, wanda ya fadi a sume, zuwa wani asibiti mafi kusa kafin daga bisani a garzaya da shi zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya (FMC) dake Owerri a motar daukan marasa lafiya.

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi: PDP ta lallasa APC a Kaduna da Bauchi, APC ta yi nasara a Cross River

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo, Orlando Ikeokwu, ya shaida wa Punch cewa rundunar 'yan sanda ta samu rahoton faruwar lamarin kuma zata fitar da sanarwa da zarar sun kammala bincike.

Daya daga cikin hadiman dan takarar ya sanar da Punch cewa likitoci suna kokarin ceton ran maigidan nasa a FMC Owerri har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel