Sanatoci sun ce ba su da masaniyar abin da kasafin kudin Majalisa ya kunsa

Sanatoci sun ce ba su da masaniyar abin da kasafin kudin Majalisa ya kunsa

Wasu daga cikin Sanatocin da ke Najeriya, sun bayyana cewa ba su san abin da ke cikin kasafin kudin majalisa na wannan shekarar ba.

Sanata Ibrahim Hadejia wanda ke wakiltar Arewa maso Gabashin Jigawa a majalisa dattawa, ya ce bai da labarin komai a game da kasafin.

Ibrahim Hadejia ya bayyana wannan ne sa’ilin da aka yi masa tambaya game da kundin kasafin Majalisar tarayya da aka saba aikinsa a boye.

“Ba ni da labarin cewa jama’a ba su san abin da ya kunsa ba ba. Ba sanin wannan bane ya kawo maganar kudin da za a kashe a gyaran majalisa?”

"Da ace ba a bayyana kasafin kudin Majalisar ba, da ta ina mutane za su san wannan (za a kashe Naira biliyan 38 wajen gyaran ginin Majalisa)?"

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ke kan teburin 'Yan majalisa bana

"A game da kasafin kudin majalisa, babu labarin abin da ya kunsa, kuma ban sani ba. Ba zan iya fada maku abin da ba da ni aka shirya ba.”

“Wannan abu ne da ya kamata ku karkatar da tambayarku ga wadanda su ka fi cancanta. Ku samu kwamitin kasafi, su ne ke da sani.” Inji sa.

Sanatan ya ce wasu Sanatoci ne su ka samu damar zama su tsara kasafin kudin ‘Yan majalisar na wannan shekarar, wanda ya ce ba ya cikinsu.

Shi ma Sanata Godiya Akwashiki na APC ya ce Akawun Majalisa ne yake da wannan bayani domin ta wurinsa duk wasu kudi su ke fita.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel