NIS: Jami’an Najeriya sun hana wasu ‘Yan Mata fita zuwa kasashen waje babu dalili

NIS: Jami’an Najeriya sun hana wasu ‘Yan Mata fita zuwa kasashen waje babu dalili

Dakarun hukumar NIS masu kula da shiga da fice a Najeriya sun hana wasu Mata barin Najeriya a babban filin jirgin saman kasar da ke Garin Legas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an tsare wadannan Mata a filin tashin jirgin Murtala Muhammed ne da ke Legas a cikin kwanakin nan.

Ana zargin cewa ana safarar wadannan Mata ne zuwa manyan Biranen Duniya irin su Lebanon, Masar, Dubai, da kasar Indiya domin su yi barna.

Hudu daga cikin wadannan mata sun bayyana cewa za su tafi wurin aikinsu ne a kasar waje, amma ba su iya fadin ainihin inda su ke aikin ba.

Bayan binciken da jami’an NIS su ka yi, an gano cewa asali ma wadannan Mata ba su san yanayin aikin da su ke ikirarin sun samu ba.

KU KARANTA: Zazzabin Lassa ta kashe mutane kusan 30 a Jihohin Najeriya

NIS: Jami’an Najeriya sun hana wasu ‘Yan Mata fita zuwa kasashen waje babu dalili
Gwamnan Najeriya tare da wasu Jami'an hukumar NIS
Asali: Facebook

Hukumar NIS ta kasa, ta bakin Mai magana da yawunta, ta bayyana cewa wasu Dillalai ne su ke daukar nauyin fitar da wadannan Bayin Allah.

Sunday James wanda ya ke magana a madadin NIS ya ke cewa Mata biyu sun fadi gaskiya da cewa mugun aiki zai fitar da su zuwa Birnin Dubai.

Sauran Matan buyu sun yi karyar cewa za su je ganin Likita ne a kasar Indiya, amma babu wasu takardu daga hukumar asibiti da su ka gabatar.

Shugaban hukumar NIS, Muhammad Babandede, ya gargadi Iyaye da su rika bi a hankali wajen sakin ‘Ya ‘yansu, ka da su afkawa hadari a waje.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel