Shugaba Trump zai hana masu zuwa Amurka haihuwa shiga kasar
- Kasar Amurka ta ce daga yanzu ba za ta kara bai wa baki 'yan kasashen waje da ke zuwa haihuwa cikinta izinin shiga kasar ba
- Ma' aikatar cikin gida ta kasar ta bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar yau Juma'a 24 ga watan Janairu
- Daga yanzu matan da ke neman izinin shiga kasar a matsayin baki sai sun nuna wata hujja mai karfi ta son zuwa Amurkan maimakon son haihuwa a can
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa kasar Amurka ta ce daga yanzu ba za ta kara bai wa baki 'yan kasashen waje da ke zuwa haihuwa cikinta izinin shiga kasar ba.
A wani jawabi daga ma'aikatar cikin gida ta kasar, ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar yau Juma'a 24 ga watan Janairu.
Saboda haka daga yanzu matan da ke neman izinin shiga kasar a matsayin baki sai sun nuna wata hujja mai karfi ta son zuwa Amurkan maimakon son haihuwa a can.
Mata musamman na Najeriya da dama sun mayar da Amurka wajen zuwa haihuwa domin samar wa 'ya'yansu takardun zama 'yan kasa.
KU KARANTA KUMA: Wani bawan Allah ya tsinci naira miliyan 9.7 a ATM sai ya mayar dashi cikin banki
Wannan lamari dai ya fara janyo muhawara sosai a shafukn sada zumuntar Najeriya
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng