Shugabar matan Kannywood ta kare jarumai mata da ke yawon bude ido a kasashen waje

Shugabar matan Kannywood ta kare jarumai mata da ke yawon bude ido a kasashen waje

Shugabar kungiyar matan masana’artar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Hauwa A. Bello, ta kare 'yan'uwanta jarumai mata wadanda ke zuwa yawon bude ido a kasashen waje, inda ta ce kallon da ake yi masu ba haka ba ne.

Hauwa ta yi martani ne ga wani rahoto da mujallar Fim ta buga a makon jiya mai taken "Ina Matan Kannywood Ke Samun Kuɗi Su Na Zarya A Ƙasashen Waje?"

A rahoton, mujallar ta yi raddi kan yadda ake ganin wasu yan kadan daga cikin fitattun jarumai mata su na yawace-yawace a kasashen waje da sunan yawon bude ido ko zuwa Umrah, inda ta yi ayar tambaya kan inda su ke samo makudan kudaden da su ke kashewa a tafiye-tafiyen bayan kuma yanzu ba fim su ke sosai ba.

Irin wadannan jaruman sun haɗa da Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi, Fati Washa, Maryam Yahaya, da sauran su, inda suke zuwa kasashe irinsu Amurka, Ingila, Faransa, Cyprus, Indiya, Dubai, Saudiyya, Masar, da sauran su.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da harkar fim ba ta ci saboda lalacewar kasuwa, babu mai samun wani abin a zo a gani.

A martanin nata wanda Mujallar fim ta ruwaito, Hauwa ce, "Su na da hanyoyin samun kuɗi duk da cewar a yanzu harkar kasuwar finafinai ta na cikin wani yanayi na durƙushewa, a sakamakon halin da kasar ta ke ciki."

Ta ce ba shakka ba daga harkar fim jaruman ke samun manyan kuɗaɗe ba.

Shugabar, wadda aka fi sani da Hauwa Edita, ta ce waɗannan jaruman su na samun talla daga manyan kamfanoni, kuma an koyar da su yadda za su caji maƙudan kuɗi a kan kowace talla.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya fara biyan karancin albashi N30,000 a Borno – Kungiyar kwadago ta tabbatar

Ta yi nuni da cewa kamar Hadiza Gabon da aka bada misali da ita, ai ta na tallar kamfanoni irin na su Ɗangote, ta ce, "To nawa ta ke samu a wannan tallar?"

Haka kuma ta ce 'yan fim din sun yi tallar 'yan siyasa a zaben da aka yi bara, don haka idan sun je yawon shakatawa ai don su na samun kudin ne.

Ta kara da cewa, "Ko da aka ce su na yawan fita, to sau nawa su ke fitan? Ai ba ko da yaushe su ke tafiyar ba; wasu ma sai shekara-shekara su ke zuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng