Yan bindiga na kashe mutanena a kullun ba tare da gwamnati ta dauki mataki ba – Sanata Sani Musa

Yan bindiga na kashe mutanena a kullun ba tare da gwamnati ta dauki mataki ba – Sanata Sani Musa

Sanata Mohammed Sani Musa, mai wakiltan Niger ta gabas daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kuma kokawa kan cewa yan bindiga na kashe mutanensa a kullun ba tare da hukumomin da ya kamata sun dauki mataki ba.

Ya yi korafin cewa duk da kiraye-kiraye daban-daban da kuma rokon da aka yiwa hukumomin da ya dace domin daukar mataki kan lamarin, ba a yi wani kokari ba sosai, kamar yadda ya ce an tursasa shi datse tafiyarsa bayan ya samu labarin sabbin hare-hare da yan bindigan suka kaddamar.

Sanata Musa wanda ya koka biyo bayan sabbin hare-haren da yan bindiga sukakai kan sama da garuruwa takwas a kananan hukumomin Shiroro da Munya tsawon kwanaki sama da biyar, ya kuma koka kan halin karin yunwa da mutanen garuruwan da lamarin ya shafa ke ciki.

Dan majalisar wanda ya koka kan yadda ake kashe mutanensa, ya bayyana cewa kisan kiyashin da yan bindiga ke yi a mazabarshi na cigaba da rusa garuruwan da ke kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya na jihar Niger.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a wani jawabi da sanatan ya sanya hannu, ya yi korafin cewa duk da rook da kukan da ya yi tare da mutanensa, laamarin na ci gaba yayinda yan bindiga ke kacin karensu ba babbaka a kan mutanen.

KU KARANTA KUMA: Tubabbun 'yan bindigan Zamfara sun nemi afuwa

Sanata Musa ya sake rokon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar da dukkanin shugabannin tsaron kasar da su kawo mafiota mai dorewa kan wannan annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel