Kamar karya: Maza kala-kala matata ke kaiwa gadonmu na sunnah - Miji ya koka

Kamar karya: Maza kala-kala matata ke kaiwa gadonmu na sunnah - Miji ya koka

- Wani dan kasuwa mazaunin Ibadan mai suna Malam Murtala Salawudeen ya bukaci kotu da ta tsinke auren shi mai shekaru 11

- Magidancin ya zargi matar shi da cin amana tare da barazana ga rayuwar shi kacokan

- Ya ce tana kawo kattai har cikin gidansu kuma kan gadonsu na aure don ya taba kama wasikar wani yana kwatanta dadin da ta shayar da shi

Wani dan kasuwa mazaunin Ibadan mai suna Malam Muritala Salawudeen ya roki kotu da ta tsinke igiyar auren shi da matar shi mai suna Adeola saboda cin amanar shi da kuma barazana ga rayuwar shi da ta ke yi, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.

A yayin bada shaida a kotun, Murtala mazaunin yankin Omiadio na Ibadan ya zargi Adeola matar shi ta shekaru 11 da cin amana, naci da rashin girmama shi.

"Rayuwata na cikin hatsari. Tana kawo maza kala-kala har cikin gidanmu. Da na mai shekaru 10 ya sanar dani cewa wani mutum mai suna Biodun na zuwa da dare duk lokutan da na yi balaguron kasuwanci na.

KU KARANTA: Makiyaya guda 4 sun yiwa wasu mata guda 4 fyade a lokaci daya

"Yaron ya sanar da ni cewa mutumin na tafiya ne da sassafe bayan ya kwanta da maman shi a gado daya. Abu mafi muni shi ne ranar da na dawo daga tafiya na tarar da wasika daga Biodun yana bayani dadin da matata ta shayar da shi."

"A halin yanzu, Adeola ta kwashe kadarorinmu masu yawa kuma ta rufe gidan ta tafi da makullin. A takaice dai Adeola ta yi min barazana da adda a lokacin da na tinkareta", ya zarga.

Adeola ta musanta don ta ce mijinta fitinanne ne mai wuyar sha'ani.

"Ban dauka komai ba kuma makullin gidan ya bace ne lokacin da ya yi min duka."

A yayin yanke hukunci, alkali Ademola Odunade ya tsinke igiyar auren tare da ba mahaifiyar rikon yaran uku da suka haifa.

Ya umarci mai kara da ya dinga biyanta alawus na N15,000 duk wata don kula dasu, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel