Takunkumin ziyara: Ba za mu yi aiki da jita-jita ba Inji Fadar Shugaban kasa

Takunkumin ziyara: Ba za mu yi aiki da jita-jita ba Inji Fadar Shugaban kasa

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta dakata ta ga matakin da shugaba Donald Trump na Amurka zai dauka game da hana mutanenta zuwa kasar wajen.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari watau Garba Shehu, ya fito ya yi magana a karon farko, inda ya ce ba za su sa baki ba tukuna.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta maida martani ga jita-jitar da ke yawo ba. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan dazu.

“Eh mun karanta a kafafen yada labarai cewa gwamnatin Trump za ta sa wasu kasashen Afrika da na Gabashin Asiya a cikin kasashen da za ta yi wa takunkumi.”

KU KARANTA: Tunawa da hadarin jirgin saman da ya rutsa da Kano a 1973

Takunkumin ziyara: Ba za mu yi aiki da jita-jita ba Inji Fadar Shugaban kasa
Ana tunanin Donald Trump zai hana 'Yan Najeriya kai wa Amurka ziyara
Asali: Facebook

“Ba za mu maida martani ga jita-jita ba. Mu na kira ku dakata mu ga yadda abubuwa za su kasance a sababbin tsare-tsaren da ake yi.” Inji Garba Shehu.

Mai magana da bakin shugaban Najeriyar ya ce za su yi la’akari da tasiri da yanayin shirin da kasar Amurka za ta fito da shi kafin shugaban kasar ya yi magana.

Rahotanni daga The Wall Street Journal sun bayyana cewa Trump na neman sa Najeriya cikin jerin kasashe bakwai da ya haramtawa shigowa kasar Amurka.

Sabon takunkumin da ake jita-jitar za a sa za ta yi aiki ne a kan Kasashen Duniya irinsu Belarus, Eritrea, Kyrgyzstan, Myanmar, Sudan, Tanzania da Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng