Mutum 3 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa a Kano, wasu a Ondo

Mutum 3 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa a Kano, wasu a Ondo

Ana kara samun yawan wadanda cutar zazzabin Lassa ta kashe. Yanzu adadin wadanda su ka rasu a dalilin cutar sun kai mutum uku a jihar Kano.

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar a Ranar 23 ga Watan Junairun 2020, ya bayyana cewa akwai marasa lafiya da yanzu ake kaffa-kaffa da su.

Akalla marasa lafiya 292 ne a Kano Likitoci su ke binsu a hankali domin zargin su na iya zama dauke da cutan. A Kano an rasa Likitoci har biyu.

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa an samu wani maras lafiya da cutar ta kashe shi a cikin makon nan, bayan wadanda su ka rasu a baya.

Kwamishinan lafiya, ya ce akwai Likitoci biyu da Ungonzoma guda da ake zargin sun kamu da cutar, yanzu za a yi masu gwaji domin a tabbatar.

KU KARANTA: Hayaki ya turnuke wasu mutane sun mutu a Garin Kaduna

Mutum 3 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa a Kano, wasu a Ondo
Ana lura mutum kusan 300 da ake zargin su na dauke da Lassa a Kano
Asali: UGC

Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa wanda shi ne Kwamishinan lafiya na jihar Kano ya yi magana a game da wanda cutar ta kashe a kwanan nan.

A cewarsa, wata Baiwar Allah ce ‘Yar shekara 28 a Duniya wanda ta ke dauke da juna biyu. Marigayiyar ta fito ne daga Yankin Gwale a jihar.

Daga wani asibitin kudi ne aka tura wannan Mata zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano, amma bayan kwana daya rak sai ta riga mu gidan gaskiya.

Ibrahim Tsanyawa ya ce sun ware mutane 292 wadanda Likitoci na musamman su ke lura da su. Ana zargin cutar ta ci mutane da yawa a jihar Ondo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel